Ana Cikin Jimamin Kisan Sojoji a Delta, Shugaba Tinubu Ya Yi Buda Baki da Hafsoshin Tsaro

Ana Cikin Jimamin Kisan Sojoji a Delta, Shugaba Tinubu Ya Yi Buda Baki da Hafsoshin Tsaro

  • Hafsoshin tsaro sun amsa gayyatar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zuwa fadarsa da ke Aso Rock Villa a Abuja
  • Shugaban ƙasar ya yi buɗa baki tare da hafsoshin tsaron ne a sabon babban ɗakin taro na Banquet Hall da ke cikin fadar shugaban ƙasa
  • Mambobin majalisar zartaswa ta tarayya da shugabannin ma'aikatu da hukumomi na daga cikin waɗanda aka yi buɗa bakin tare da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya karɓi baƙuncin hafsoshin tsaron domin buɗa bakin azumin watan Ramadan a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Ɓuɗa bakin na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da kace-nace kan kisan da aka yi wa sojoji 16 a jihar Delta a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, 2024.

Kara karanta wannan

Murna yayin da Shugaba Tinubu ya fadi lokacin da tsadar rayuwa za ta kare a Najeriya

Tinubu ya yi buda baki da hafsoshin tsaro
Shugaba Tinubu ya yi buda baki tare da hafsoshin tsaro Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Su wa Tinubu ya yi buɗa baki da su?

Shugaban ƙasan ya kuma karɓi baƙuncin mambobin majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), shugabannin ma’aikatu da hukumomi, a fadarsa da ke Abuja a ranar Talata, 19 ga watan Maris, domin buɗa baki a watan Ramadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mambobin majalisar ministoci da dama sun taru a cikin sabon ɗakin taro na Banquet dake fadar shugaban ƙasa domin buɗa baki tare da Shugaba Tinubu, cewar rahoton jaridar The Nation.

A ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, shugaban kasar ya karɓi baƙuncin gwamnonin 36 na ƙasar nan, jim kaɗan bayan kashe sojoji 16 a yankin Okuama dake jihar Delta.

Ƴan bindigan a yayin harin sun kashe Kwamanda ɗaya, Manjo biyu, Kyaftin ɗaya da sojoji 12 bayan sun yi musu kwanton ɓauna.

Shugaba Tinubu ya gana da Oberevwori

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu: Kotu ta yi hukunci kan shari'ar shugaban kungiyar IPOB

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oberovwori a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja.

Gwamnan ya ziyarci shugaban ƙasan kan ta'adin da aka yi na halaka sojoji 16 a yankin Okuama na ƙaramar hukumar Ughelli ta jihar.

Gwamnan a yayin ziyarar ya yi wa shugaban ƙasan cikakken bayani kan yadda lamarin mara daɗi ya auku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel