Mataki Mai Karfi da Hukumar Soji Ta Dauka a Delta Bayan Kashe Mata Jami’ai 16

Mataki Mai Karfi da Hukumar Soji Ta Dauka a Delta Bayan Kashe Mata Jami’ai 16

  • Rundunar sojin Najeriya na neman wadanda ake zargin sun kashe jami’anta a yankin karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta
  • Rundunar ta kuma tura karin sojoji domin ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya, tare da ruguza wasu gine-gine a garin Okuoma
  • Ba ta tsaya a jihar Delta kadai ba, rundunar soji ta fadada neman wadanda ake zargin, zuwa garuruwan Bayelsa inda ake zargin sun fake

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Rahotannin sun bayyana cewa wasu sojoji dauke da mugayen makamai sun mamaye yankunan gabar tekun jihohin Bayelsa da Delta a ranar Lahadi, 18 ga watan Maris.

An ruwaito cewa sojojin na daga cikin karin dakarun da aka tura yankin ne domin kamo wadanda suka kashe sojojin Najeriya sama da 16 a Delta.

Kara karanta wannan

Zamfara: Sojojin Najeriya sun halaka wani shugaban ƴan bindiga da mayakansa

Rundunar soji ta dauki mataki kan wadanda suka kashe sojoji a Delta
Delta: Sojoji sun fadada neman wadanda a kashe jami'ansu sama da 20. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Yadda mutanen Delta suka kashe sojoji

A baya Legit ta rahoto cewa wasu mutane dauke da bindiga sun kashe sojoji da dama a kauyen Okuoma da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar, 16 ga Maris.

Daraktan yada labarai na tsaro, Tukur Gusau, ya ce wasu matasa a karamar hukumar Bomadi ta jihar Delta dauke da makamai suka kashe sojojin bayan sun kewaye su.

Sojoji sun dauki mataki mai tsauri

An tattaro cewa an girke sojoji a yankunan da abun ya faru da sauran garuruwan Ijaw da Urhobo da ke makwabtaka da juna a jihohin Delta da Bayelsa.

Da yake magana kan lamarin, wata majiyar tsaro ta bayyanawa jaridar Leadership cewa, an kuma jibge jiragen ruwa guda shida na yaki a tekun garin Okuama.

Kara karanta wannan

Kaduna: Rundunar soji ta samu gagarumar nasara bayan ceto mutane 16 hannun miyagu

Tuni dai an tattaro cewa hukumomin soji sun rubuta sunayen ’yan ta'addan da suka aikata wannan danyen aikin domin a kama su.

Shugaban Sojoji zai ziyarci yankin Delta

Rahoton Arise News ya nuna cewa a yau litinin 18 ga watan Maris ne ake sa ran babban hafsan sojin kasa (CoAS), Laftanan Taoreed Lagbaja, zai ziyarci garin da lamarin ya faru.

Rahotanni sun ce sojoji sun fara aiki kan bayanan da suka samu na cewa wadanda ke da hannu wajen aikata kisan sun tsere zuwa wasu garuruwa a jihar Bayelsa.

Bugu da kari, jaridar Vanguard ta ce za a ayyana wani sanannen tsohon shugaban tsageru da kungiyarsa a matsayin wadanda ake tuhuma da aikata kisan.

Kisan sojoji: Tinubu, majalisa sun yi martani

Tun da fari, Legit ta ruwaito cewa shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu ya yi Allah wadai da kashe sojojin da aka yi a jihar Delta tare da ba da umarnin kamo wadanda suka aikata laifin.

Haka zalika, ita ma majalisar dattawa, ta ba rundunar soji umarnin yin duk mai yiwuwa domin ganin an kamo wadanda suka kashe sojojin tare da hukunta su ba tare da jinkiri ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel