Okuama: Bola Tinubu Ya Gana da Gwamnan PDP Kan Kisan Sojoji 17, Sahihan Bayanai Sun Fito

Okuama: Bola Tinubu Ya Gana da Gwamnan PDP Kan Kisan Sojoji 17, Sahihan Bayanai Sun Fito

  • Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnan jihar Delta a fadar shugaban kasa kan mummunan lamarin da ya yi ajalin sojoji
  • Jim kaɗan bayan ganawarsu, Gwamna Oborevwori ya tabbatar da cewa duk mai hannu a kisan gillan da aka yi wa sojojin zai ɗanɗana kuɗarsa
  • Ya ce tuni ya gana da shugabannin tsaro amma har yanzun bai samu damar zama da mutanen yankin ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya karbi bakuncin Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Talata.

Gwamna Oborevwori ya yi wa Shugaba Tinubu cikakken bayanin abin da ya faru wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji 17 a kauyen Okuama, ƙaramar hukumar Ughelli a Delta.

Kara karanta wannan

A karo na biyu, gwamnan Arewa ya fara raba tallafin kuɗi da abinci na N11.4bn a jiharsa

Shugaba Tinubu.
Gwamnan Delta ya yi wa Tinubu bayanain abin da ya faru Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Oborevwori ne ya bayyana haka yayin hira da ƴan jaridar gidan gwamnati jim kaɗan bayan kammala tattaunawa da Bola Tinubu, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane hali ake ciki a Okuama a yanzu?

Ya ce an shawo kan lamarin yanzu, sannan ya ba da tabbacin cewa za a zaƙulo wadanda suka yi wa sojojin kisan gilla a lamarin tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Gwamnan ya kuma ƙara tabbatarwa ƴan Najeriya cewa ba za a sake samun afkuwar irin wannan mummunan lamarin ba a yankinsa, rahoton Guardian.

Haka nan kuma ya ce gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa ba a haɗa da waɗanda ba ruwansu ba wajen hukunta waɗannan miyagu.

Gwamnan ya ƙi faɗin ainihin alkaluman adadin wadanda suka mutu, yana mai cewa kasancewar lamarin ya shafi matsalar tsaro, akwai wasu abubuwa da ba zai iya fada a cikin jama’a ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gana da ƴan takara 2 da ƙusoshin APC kan muhimmin batu a Villa, bayanai sun fito

Oborevwori ya gana da shugabannin tsaro

Ya ce ya gana da shugabannin hukumomin tsaro a Bomadi ranar Litinin amma bai samu zama da al’ummar da abin ya shafa ba saboda gaba daya wurin ba kowa a yanzu.

A jiya ne hedkwatar tsaro ta fitar da jerin sunaye da hotunan dakarun sojojin da aka kashe a jihar Delta.

Tinubu na shirin rabuwa da wasu ministoci

A wani rahoton kuma matsala ta kunno kai ga ministocin da ke karkashin gwamnatin Bola Tinubu wadanda ba su aiwatar da aikin da aka dora masu ba

Wasu majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun bayyana cewa shugaban na shirin rabuwa da dukkan ministocin da suka gaza taɓuka komai

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel