Murna Yayin da Shugaba Tinubu Ya Fadi Lokacin da Tsadar Rayuwa Za Ta Kare a Najeriya

Murna Yayin da Shugaba Tinubu Ya Fadi Lokacin da Tsadar Rayuwa Za Ta Kare a Najeriya

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi buɗa baki tare da ministoci da hafsoshin tsaro a fadarsa da ke Aso Rock Villa
  • A wajen shan ruwan na azumin Ramadan, Tinubu ya ce nan bada jimawa ba matsalar taɓarɓarewa tattalin arziƙi za ta zama tarihi
  • Shugaban ya buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da addu'o'i domin samun zaman lafiya da ƙwanciyar hankali mai ɗorewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu a ranar Talata, 19 ga watan Maris, 2024, ya ce tattalin arziƙin Najeriya ya kama hanyar farfaɗowa.

Jaridar The Punch, ta kawo rahoto cewa Tinubu ya yi alƙawarin cewa ƴan Najeriya za su sake yin murmushi a cikin watanni masu zuwa.

Kara karanta wannan

Ana cikin jimamin kisan sojoji a Delta, Shugaba Tinubu ya yi buda baki da hafsoshin tsaro

Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya albishir
Shugaba Tinubu na kokarin shawo kan matsalar tattalin arziki Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Ya yi nuni da cewa, wasu ƙasashe sun fuskanci taɓarɓarewar tattalin arziki fiye da wanda Najeriya ta samu a watannin baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu, wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi bakuncin ministoci, hafsoshin tsaro da sauran manyan jami’an gwamnati domin buɗa baki a watan Ramadan.

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa an yi buɗa bakin ne a ɗakin taro na Banquet Hall da ke cikin fadar Aso Rock Villa.

Wane ƙoƙari Shugaba Tinubu yake yi?

A kalamansa:

"Cikin sa'a tattalin arziƙin ya fara farfaɗowa. Da yardar Allah a cikin watanni masu zuwa, za mu samu lokacin girbi mai albarka, kuma za mu sake yin murmushi.
"Masu girma ministoci, hafsoshin tsaro, mun tsallake lokacin wuya sannan yanzu ƙasar nan na kan hanyar samun ci gaba mai ɗorewa. Wasu ƙasashen sun fuskanci abin da yafi haka muni a tarihinsu fiye da mu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gana da ƴan takara 2 da ƙusoshin APC kan muhimmin batu a Villa, bayanai sun fito

"Shugaban ƙasa yana aiki tuƙuru domin ƙasar nan. Yana da zuciya mai kyau don ci gaban ƙasar nan sannan muna da alhakin mara masa baya da duk hanyar da za mu iya domin ya ceto ƙasar nan.

Da yake bayyana watan Ramadan a matsayin lokacin yafiya da nuna halin kirki, Tinubu ya yi kira da a yi addu’o’i domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar nan.

Tinubu ya yi sababbin naɗe-naɗe

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa tawagar da za ta ja ragamar hukumar kula da almajirai da yaran da ba su zuwa makaranta.

Shugaban ƙasan ya nada Birgediya Janar Lawal Jafaru Isa a matsayin babban shugaban hukumar ta ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel