APC Ta Nemi Gwamna Mutfwang Ya Fice Daga PDP, Ta Zayyana Masa Manyan Dalilai

APC Ta Nemi Gwamna Mutfwang Ya Fice Daga PDP, Ta Zayyana Masa Manyan Dalilai

  • An yi kira ga gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang da ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC domin ya daga darajarsa
  • Kungiyar APC ta Arewa ta tsakiya ce ta yi wannan kiran a ranar Laraba a Jos, tana mai cewa akwai bukatar Mutfwang ya hada kai da Tinubu
  • A cewar shugaban kungiyar, Saleh Mandung Zazzaga, Mutfwang ba zai iya cimma muradunsa a PDP ba, har sai ya hada hannu da jam'iyyar tsintsiya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jos, jihar Filato - An nemi Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato da ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC domin ya kara samun daraja a idon al'umma.

Kara karanta wannan

Bayan katobara a zaman makoki, gwamnan PDP ya sake shiga matsala kan bukatar APC a jihar

Kungiyar APC ta Arewa maso tsakiya ce ta yi wannan kiran a ranar Laraba a Jos, babban birnin jihar Filato, a wajen taronta na farko na shekarar 2024.

APC na neman Mutfwang ya bar PDP
APC ta zayyana wa Gwamna Mutfwang dalilan da za su sa ya ya fice daga PDP. Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban kungiyar, Saleh Mandung Zazzaga, ya ce sun yi taron ne domin duba halin da jam’iyyar ke ciki da kuma tattalin arziki da tsaro a shiyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manufar sauya shekar Mutfwang daga PDP - Zazzaga

Saleh Zazzaga ya kara da cewa gwamnan jihar filato na da matukar muhimmanci wajen ci gaban shiyyar baki daya, saboda haka suke fatan ya koma APC.

Zazzaga, wanda kuma mamba ne a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a zaben da ya gabata, ya yabawa Gwamna Mutfwang bisa yadda ya ke tafiya da kowa a mulkinsa.

Sai dai ya ce idan har gwamnan ya na so ya samu cikar muradunsa na kawo ci gaba mai dorewa a jihar Filato, to sai ya sauya sheka zuwa APC.

Kara karanta wannan

Zan kafa tarihi kamar Buhari, dan takarar gwamnan APC ya bugi kirji kan zabe

Ya ce gwamnan ba wai zai bar PDP da nufin ya durkusar da tsohuwar jam’iyyar ba ne ba, illa dai hakan zai kara karfafa masa gwiwa wajen bunkasa jihar Filato.

Mutfwang na son ci gaban Filato - Zazzaga

A cewar shugaban, ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, babban misali ne na wanda ke neman ci gaban al’ummarsa da kasa baki daya ba tare da la'akari da jam'iyya ba.

“Ya zuwa yanzu Gwamna Caleb Mutfwang ya nuna cewa shi gwamna ne mai son ci gaba ta hanyar maganganunsa da ayyukansa tun bayan hawansa mulki.
"Amma domin ya kara samun daraja da ci gaba, akwai bukatar ya koma APC, wanda zai ba shi damar hada kai da Shugaba Bola Tinubu wajen bunkasa jihar Filato."

- A cewar Zazzaga.

Mutfwang ya ba 'yan majalisu 16 mukami

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya ba 'yan majalisu 16 da kotu ta tsige mukamai a gwamnatinsa.

Mutfwanga ya ba 'yan majalisu mukamai na 'wakilan mazabu' da nufin zamar masa wata fitila ta haska wuraren da ya kamata a yi wa aiki a jihar ta Filato.

Asali: Legit.ng

Online view pixel