Zan Kafa Tarihi Kamar Buhari, Dan Takarar Gwamnan APC Ya Bugi Kirji Kan Zabe

Zan Kafa Tarihi Kamar Buhari, Dan Takarar Gwamnan APC Ya Bugi Kirji Kan Zabe

  • Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar Ondo, ‘yan siyasa sun fara kamfe tare da neman yardar al’ummar jihar
  • Dan takarar jam’iyyar APC a zaben jihar Ondo, Olusola Oke ya bayyana cewa lokacinsa ya yi na kasancewa gwamnan jihar
  • Oke ya ce shi a zai kafa tarihi kamar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya yi nasara a zabe bayan faduwa sau uku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo – Dan takarar gwamnan APC a jihar Ondo, Olusola Oke ya yi alfahari kan zaben jihar inda ya ce lokacinsa ya yi.

Oke na daga cikin ‘yan takara da ake ji da su a zaben da za a gudanar a wannan shekara bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu.

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki tsattsauran hukunci kan likitan bogi da ake zargin ya kashe majinyaci

Dan takarar gwamnan APC ya sha akwashin lashe zabe a karo na hudu kamar Buhari
Olusola ya ce wannan lokacinsa ne na darewa kujerar gwamnan jihar Ondo. Hoto: Olusola Oke, Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

Wace bukata Olusola ya tura ga APC?

Olusola ya bukaci kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta kasa da jihar da su gudanar da zaben cikin adalci, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar ya ce kamar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari shi ma ya yi takara har sau uku bai yi nasara ba, cewar Arise TV.

Ya ce amma a yanzu zai sake tsayawa takara a karo na hudu inda ya ce kamar Buhari wannan ita ce damarsa ta darewa kujerar.

Ya yi fatan zama kamar Buhari

“Nima kamar Buhari, nayi takara sau uku ban yi nasara ba, amma wannan karon zan yi nasarar bayan gwadawa har sau uku.”
“Mimiko ya nemi takarar gwamna daga Ondo ta Tsakiya, Akeredolu kuma Ondo ta Arewa ni kuma yanzu lokacina ne saboda za a mayar da tikitin Ondo ta Kudu yankina kenan”

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan korafin ministan Buhari kuma dan takarar gwamna a APC

“Idan ba ku manta ba mun taso mu uku a siyasance, da ni da Mimiko da kuma Akeredolu, dukkanmu mun fito daga yankuna daban-daban.”

- Olusola Oke

An fara samun rikici a gwamnatin Ondo

Kun ji cewa Matar tsohon gwamnan jihar Ondo, marigayi Rotimi Akeredolu ta soki surukarta kan goyon bayan Gwamna Lucky Aiyedatiwa.

Betty Akeredolu ta ce tabbas Funke Akeredolu wacce ‘yar uwar marigayin ne ta cika butulu kan goyon bayan gwamnan jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar a karshen wannan shekara da muke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel