Wani Hanin: 'Yan Majalisa 16 da Kotu Ta Tsige a PDP Sun Samu Manyan Muƙaman Gwamnati

Wani Hanin: 'Yan Majalisa 16 da Kotu Ta Tsige a PDP Sun Samu Manyan Muƙaman Gwamnati

  • Mambobin majalisar dokokin jihar Filato guda 16 da kotun daukaka kara ta tsige sun samu muƙamai a gwamnatin Celeb Mutfwang
  • Gwamnan ya naɗa su a matsayin jami'an hulɗa da jama'a a mazaɓunsu domin su taimaka masa wajen kawo ci gaba a faɗin jihar Filato
  • Sai dai ƴan majalisar na ta kokarin yadda zasu kwato kujerunsu bisa la'akari da hukuncin kotun koli kan nasarar Gwamna Mutfwang

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Filato - Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya nada korarrun ‘yan majalisar dokokin jiha na jam’iyyar PDP a matsayin hadimansa.

Gwamna Muftwang ya naɗa ƴan majalisu 16 waɗanda kotu ta tsige daga majalisar dokokin jihar Filato a matsayin jami'an hulɗa da jama'a a mazaɓunsu.

Kara karanta wannan

Boko Haram: Sama da 90% na ainihin masu aƙidar ta'addanci sun mutu Inji Zulum

Gwamnan jihar Filato, Celeb Mutfwang.
Gwamna Mutfwang Ya Nada Yan Majalisa 16 da Kotu Ta Tsige a Muƙami a Filato Hoto: Celeb Mutfwang
Asali: Facebook

Idan dai ba a manta ba, ‘yan majalisar 16 sun rasa kujerunsu na majalisar dokokin jihar a watan Nuwamban 2023, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa kotu ta kori ƴan majalisar Filato 16?

Sun rasa kujerunsu ne sakamakon hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke cewa jam'iyyar PDP ba ta cika sharuɗɗan tsaida ƴan takara ba a zaben 2023 ba.

Amma tun da kotun koli ta yi watsi da irin wannan hukunci da aka yanke a shari'ar Gwamna Mutfwang, 'yan majalisar suka sha alwashin ci gaba da fafutukar kwato kujerunsu.

Bayan sun je zauren majalisar a watan Janairu bayan ta dawo daga hutu, ‘yan majalisar sun kuma durfafi kotun daukaka kara domin neman ta sake duba hukuncin da ta yanke na korarsu.

A makon da ya gabata ne kotun daukaka kara ta yi watsi da karar tare da ci tarar masu kara Naira miliyan 128 saboda shigar da karan da ba ta dace ba saboda bata lokacin kotun.

Kara karanta wannan

Dattawa sun tsoma baki kan batun sojoji su kifar da Gwamnatin Shugaba Tinubu kan abu 2

Gwamna ya fara rarrashin 'yan majalisa da muƙami

A ranar Litinin, 4 ga watan Maris, Gwamnan ya rantsar da su a matsayin hadimansa, waɗanda za su taimaka masa a mazaɓunsu.

Da yake shaida rantsar da su, Mutfwang ya ce ya naɗa su ne da nufin inganta harkokin karkara da kuma samar da ci gaba mai amfani a fadin jihar, Vanguard ta rahoto.

Hisbah: Daurawa ya sasanta da Abba

Kuna da labarin Sheikh Aminu Daurawa ya koma kan muƙamin shugaban hukumar Hisbah na jihar bayan sasaantawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Hakan ya biyo bayan wata ganawa da aka yi tsakanin Gwamna Abba da tawagar malaman Kano ciki harda babban kwamandan Hisbah ranar Litinin da daddare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel