Halin Kunci: Gwamna a Arewa Ya Tausaya, Zai Raba Tirelolin Abinci 200 Kyauta Domin Rage Wahala

Halin Kunci: Gwamna a Arewa Ya Tausaya, Zai Raba Tirelolin Abinci 200 Kyauta Domin Rage Wahala

  • Yayin da ake cikin wani mawuyacin hali a Najeriya, Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya waiwayi al'ummarsa
  • Gwamnan ya sanar da shirin raba tirelolin hatsi har 200 domin rage wahalhalun da jama'a suke ciki a jihar
  • Gwamnan ya sanar da shirin aiwatar da wannan gagarumin aiki ne a yau Juma'a 8 ga watan Maris a shafinsa na X

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kebbi - Gwamna jihar Kebbi, Kwamred Nasir Idris zai raba kayan abinci ga al'ummar jihar yayin da ake cikin halin kunci.

Gwamna Idris ya ce zai raba kayan abincin ne kyauta ga bayin Allah a jihar domin rage musu radadin wahalar da ake ciki a yanzu.

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Gwamnan Ribas ya fadi abin da ya yi niyya lokacin shirin tsige shi

Gwamnan APC zai gwangwaje 'yan jiharsa da kayan abinci domin rage radadi
Gwamna Nasir Idris ya ce zai ci gaba da kawo tsare-tsare domin tallafawa jama'a. Hoto: Nasir Idris.
Asali: Facebook

Tireloli nawa gawamnan ya ce zai raba?

Gwamnan ya bayyana wannan a yau Juma'a 8 ga watan Maris a shafinsa na X inda ya ce yanzu aka fara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idris ya ce sun ware tireloli 200 na abinci musamman domin rabon, inda ya bayyana himmatuwarsa wurin kawo sauyi a halin da ake ciki.

Har ila yau, gwamnan ya sanar da injunan ban ruwa masu amfani da hasken rana da iskar gas domin inganta aikin manoma da ke jihar.

Wannan mataki a cewarsa, na daga cikin tsare-tsaren gwamnatinsa da za su inganta harkokin noma a jihar da ke Arewa maso yamma.

Idris ya himmatu wurin inganta rayuwar al'umma

"Ina farin cikin sanar da ku cewa gwamnatinmu a jihar Kebbi za ta raba tirelolin hatsari har guda 200 domin rage halin yunwa da ake ciki."

Kara karanta wannan

'Dan takarar shugaban kasa ya fadi tsawon lokacin da za a dauka kafin fita daga matsala

"Wannan kaya da gwamnatin ta samar zai taimaka wurin rage wahalar da al'ummominmu ke ciki da tsadar rayuwa."
"Gwamnatinmu ta himmatu wurin tabbatar da kawo sauyi a rayuwar al'umma da ke fadin jihar."

- Nasir Idris

Gwamna Idris ya ba 'yan majalisu motoci

Kun ji cewa Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris ya raba sababbin motoci guda 24 ga 'yan majalisar dokokin jihar.

Gwamnan ya ce ya ba da kyautar motocin ne domin saukaka ayyukan 'yan majalisar a jihar.

Wannan mataki na gwamnan ya jawo cece-kuce ganin yadda aka yi rabon motocin a lokacin da mutane ke cikin wani hali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel