Ana Tsadar Rayuwa, Gwamnan APC Ya Gwangwaje 'Yan Majalisa da Sababbin Motoci, Ya Fadi Dalili

Ana Tsadar Rayuwa, Gwamnan APC Ya Gwangwaje 'Yan Majalisa da Sababbin Motoci, Ya Fadi Dalili

  • Gwamnan jihar Kebbi ya gwangwaje ƴan majalisar dokokin jihar da motoci masu rai da lafiya domin su ji daɗin gudanar da ayyukansu
  • Gwamna Nasir Idris ya yi nuni da cewa ya ba su motocin domin jin daɗin kyakkyawar alaƙar aiki da ke a tsakaninsu
  • Ya buƙaci ƴan majalisar da su yi amfani da motocin ta hanyar da ta dace don cimma manufar da aka sayo su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya raba sababbin motoci ƙirar Toyoa Fortuner Jeep guda 24 ga ƴan majalisar dokokin jihar.

Jaridar The Punch tace yayin miƙa motocin ga ƴan majalisar a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi a ranar Talata, gwamnan ya ce motocin an bada su ne domin sauƙaƙa ayyukan ƴan majalisar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya tuna da talakawa, ya rage farashin kayan hatsi saboda azumi

'Yan majalisa sun samu motoci a Kebbi
Gwamna Idris ya raba motoci ga 'yan majalisa Hoto: @kaura_movement
Asali: Twitter

Meyasa Gwamna Nasir ya ba su sabbin motoci?

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Ahmed Idris ya rabawa manema labarai, ta bayyana cewa gwamnan ya yaba da kyakkyawar alaƙar aiki da ke tsakanin ɓangaren zartarwa da na majalisa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ci gaba da cewa, gwamnan ya ƙarfafa gwiwar ƴan majalisar da su ɗore da kyakykyawar alaƙa mai kyau domin jihar ta samu ci gaba cikin sauri, rahoton Oasismagazine ya tabbatar.

Wani ɓangare na sanarwar tana cewa:

"Dole ne in bayyana a nan cewa ina jin daɗin zaman lafiyar da ke tsakaninmu, ban taɓa samun saɓani da shugaban majalisar ba, ko wani daga cikin ƴan majalisar.
"Wannan a zahiri ya taimaka mana wajen aiwatar da ayyuka a dukkan masarautun jihar nan don amfanin mutanenmu."

Gwamnati ta raba motoci a baya

Gwamnan ya ƙara da cewa a baya ya saya tare da raba sabbin motoci guda 30 ga jami’an tsaro da guda 28 ga kwamishinonin jihar.

Kara karanta wannan

Majalisa ta yi magana kan matan da aka sace a Borno, ta tabo jami'an tsaro

Gwamna Idris ya ce gwamnatinsa ta zaɓi ba su sababbin motoci ne domin kaucewa duk wata gazawa wajen gudanar da ayyukansu.

Ya kuma buƙace su da su yi amfani da ababen hawan yadda ya kamata domin manufofin da aka sayo su domin su.

Legit Hausa ta tuntuɓi wani mazaunin jihar Kebbi mai suna, Muhammad Kamba, wanda ya nuna rashin jindaɗinsa dangane da wannan matakin da gwamnan ya ɗauka.

Ya bayyana cewa sayan motocin bai dace ba duba da yanayin halin da talakawa suke ciki na matsin rayuwa, amma an ɓishe da ƙarawa mai masu hannu da shuni ƙarfi.

A ganinsa kamata ya yi a sanya kuɗaɗen wajen da za su amfani talakawan jihar, ba a ƙarar da su wajen siyawa ƴan majalisun sabbin motoci ba.

Za a Daina Ɗauke Wuta a Kebbi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi wa jama'ar jihar alƙwarin daina ɗauke wutar lantarki a lokacin azumin watan Ramadan.

Gwamnan ya bayyana cewa tuni shirye-shirye suka kankama domin ganin mutanen jihar sun yi azumi cikin walwala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel