Kamar Kaduna, Gwamnan APC Ya Caccaki Tsoffin Gwamnoni, Ya Yi Gargadi Mai Tsauri

Kamar Kaduna, Gwamnan APC Ya Caccaki Tsoffin Gwamnoni, Ya Yi Gargadi Mai Tsauri

  • Gwamnan jihar Binuwai, Alia Hyacinth ya dauki zafi kan yadda wasu tsoffin gwamnoni ke kawo cikas a zaman lafiyar jihar
  • Gwamna ya ce kowa ya yi zamaninsa ba tare da matsala ba ya kamata a bar shi ya gudanar da mulkinsa wurin inganta rayuwar 'yan jihar
  • Alia ya ce idan har mutum komai girmansa ba zai kawo ci gaba ba to gwara ya kulle bakinsa ya yi shiru kan harkokin jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue - Gwamna Hyacinth Alia na jihar Binuwai ya gargadi tsoffin gwamnonin jihar kan tsoma baki a harkokin mulkinsa.

Alia ya ce idan har ba za su taimakawa jihar wurin samun ci gaba to su yi shiru da bakinsu su bar shi ya ci gaba da ayyukan alheri.

Kara karanta wannan

"Ku daina tsoma baki a gwamnatina" Gwamna ya gargaɗi tsofaffin gwamnoni

Gwamnan APC ya gargadi tsoffin gwamnoni kan tsoma baki a mulkinsa
Gwamna Alia Hyacinth na Binuwai ya yi gargadi ga tsoffin gwamnoni a jihar. Hoto: Alia Hyacinth.
Asali: Facebook

Ya bukaci ba shi dama a mulkinsa

Gwamna ya ce wanda suka mulki jihar a baya sun samu dama domin haka ya kamata su ba shi dama ya gudanar da mulkinsa, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hyacinth ya bayyana haka yayin ganawarsa da kungiyar magoya bayan jam'iyyar APC da suka taro shi bayan kai ziyara Amurka.

Ya ce gwamnatinsa ta himmatu wurin inganta rayuwar al'umma inda ya ce ba zai gajiya ba wurin kawo abubuwan more rayuwa a jihar.

Har ila yau, gwamnan ya gargadi masu hada baki da abokan gaba wurin kawo cikas a zaman lafiyar jihar komai girman mutum, cewar New Telegraph.

Ya gargadi tsoffin gwamnoni a jihar

"Ba zan taba yadda wani ya kawo cikas a jihar nan ba komai girmansa a cikin al'umma."
"Ko da kuwa tsohon gwamna ne idan babu abin ci gaba da zai kawowa jihar ya rufe bakinsa."

Kara karanta wannan

Badakalar $720, 000: Yadda muka yi da tsohon gwamna Yahaya Bello Inji Shugaban EFCC

"Saboda kowa ya yi zamaninsa yanzu ya kamata a ba da kofa ga zaman lafiya domin samarwa 'yan jihar ababan more rayuwa."

- Alia Hyacinth

Gwamna Sanwo-Olu ya rufe wuraren ibada

A wani labarin, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya umarci rufe wasu coci-coci guda biyar da wuraren shakatawa 19 a jihar.

Gwamnatin jihar ta dauki wannan matakin ne yayin da aka zarge su da laifin damun al'umma da kararraki wanda ya sabawa doka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel