Wike vs Fubara: Gwamnan Ribas Ya Fadi Abin da Ya Yi Niyya Lokacin Shirin Tsige Shi

Wike vs Fubara: Gwamnan Ribas Ya Fadi Abin da Ya Yi Niyya Lokacin Shirin Tsige Shi

  • Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya yi magana a kan rikicin siyasar da ya dabaibaye shi da magabacinsa, Nyesom Wike
  • Fubara ya ce a shirye yake ya bar muƙaminsa na gwamna domin samun zaman lafiya a jihar ta yankin Kudu maso Kudu na Najeriya
  • Gwamnan ya bayyana cewa da bai tunkari batun tsige shi da dattaku ba, da rikicin da ya dabaibaye jihar a watannin baya ya yi muni

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Fatakwal, jihar Ribas - Gwamna Siminalayi Fubara ya ce da ya yi amfani da dukkan ƙarfin ikonsa a matsayinsa na gwamnan jihar Ribas, da an samu rikici a jihar.

Fubara ya bayyana haka ne a wata hira da aka sanya a shafin X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) na gidan talabijin ɗin AIT a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

"Saura ƙiris ku ji daɗi" Shugaba Tinubu ya aika saƙo ga ƴan Najeriya, ya kaddamar da sabon shiri

Fubara ya magantu kan rikicinsa da Wike
Gwamna Fubara yana takun saka tsakaninsa da Nyesom Wike Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana cewa bai cika damuwa da rasa kujerarsa ba, amma ya damu da ƴan asalin jihar Ribas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Fubara zai iya haƙura da mulki

Gwamnan na jam’iyyar PDP ya bayyana cewa:

"Abin da na damu da shi a wancan lokacin ba maganar dukkan wasan kwaikwayon nan ba ne. Na damu ne da miliyoyin mutanen Ribas waɗanda suka yi sadaukarwa, waɗanda suka ga dama ta samu amma ta yi kamar tana ƙoƙarin suɓuce musu.
"Saboda su ne na damu, me makomarsu za ta kasance? Wannan ita ce matsalar ba saboda kai na ba ne."

Bugu da ƙari, Gwamna Fubara ya bayyana cewa idan barin mulki shi ne abin da ake buƙata don samar da zaman lafiya a jihar Ribas, a shirye yake ya rasa kujerarsa.

A kalamansa:

"Ya kamata mutane su gane cewa ba wai saboda ni ba ne. Tabbas, zan tafi, amma jihar Ribas za ta ci gaba da zama."

Kara karanta wannan

Ana ba tsaro a kasa, Akpabio ya fito ya fadi ci gaban da Tinubu ya kawo a bangaren

'Dalilin yin sulhu da Wike' - Gwamna Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta shiga cikin wani ƙazamin yaƙin siyasa da zai kawo cikas ga cigaban jihar ba.

Ya kuma bayyana cewa matakin da gwamnatinsa ta ɗauka a rikicin siyasar jihar ba don tsoro ba ne, sai domin a samu zaman lafiya a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel