'Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Fadi Tsawon Lokacin da Za a Dauka Kafin Fita Daga Matsala

'Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Fadi Tsawon Lokacin da Za a Dauka Kafin Fita Daga Matsala

  • Yayin da ake cikin halin kunci, da alamu za a dade ana jin jiki bayan tsohon mataimakin gwamnan CBN ya yi magana
  • Farfesa Kingsley Moghalu wanda ya yi takarar shugaban kasa ya ce tabbas za a dade ana cikin wannan halin
  • Moghalu ya ce dukkan wadannan matsalolin sun faru ne saboda yadda aka gudanar da kasar cikin rashin kwarewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa, Farfesa Kingskey Moghalu ya ce aƙalla sai an yi shekaru uku zuwa biyar ana shan wahala da ake ciki.

Dan siyasar kuma masanin tattalin arzikin ya ce hakan ya faru ne saboda cin hanci da kuma tsare-tsare marasa kan gado, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Fitaccen basarake ya tura sako ga Tinubu kan kafa hukumar kayyade farashi

Tsohon mataimakin bankin CBN ya yi magana kan halin da ake ciki
Moghalu ya ce za a shafe shekaru 5 ana cikin wannan kunci. Hoto: Kingsley Moghalu.
Asali: UGC

Menene Moghalu ya ce kan halin da ake ciki?

Tsohon mataimakin gwamnan CBN ya bayyana haka ne a jiya Talata 5 ga watan Maris a Abuja yayin wani taron ba da lambar yabo daga jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Moghalu ya ce dukkan wadannan matsaloli sun faru ne saboda matakan da aka dauka a baya marasa kyau.

Ya ce dukkan matsalolin da suka hada da tsadar kaya da faduwar naira da rashin aikin yi sun samu ne yadda ake gudanar da tattalin arzikin kasar na tsawon lokaci.

“Shekaru 10 da suka wuce aka nakasa tattalin arzikin kasar wurin rashin iya tsare-tsare da karban basuka da kuma gibi a kasafin kudade.
“Sannan tsare-tsaren bankin CBN wurin daidaita tsarin cinikayyar kudaden kasar waje da naira ya taimaka wurin nakasu a tattalin arziki har sau biyu a shekaru bakwai.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta bayyana ainihin abin da ya jawo karancin abinci da tsadar rayuwa

“Tabbas wannan kura-kurai da aka tafka zai iya daukarmu shekaru uku zuwa biyar kafin samun damar dakile su.”

- Kingley Moghalu

Shawarar da Moghalu ya bayar

Bangaren cire tallafin mai, Moghalu ya ce wannan mataki ya yi dai-dai kuma an yi shi cikin karfin hali, cewar rahoton The Nation.

Sai dai ya kushe tsarin gwamnatin wurin aiwatar da tsare-tsaren ba tare da wayar da kan jama’a kan matakan ba kafin aiwatar da su.

“Ya kamata a wayar da kan ‘yan Najeriya kan dalilin cire tallafin da kuma amfanin cirewar da kuma tsarin da zai rage wa mutane wahalhalu.”

- Kingsley Moghalu

Kwastam ta kama wake buhunan 400

Kun ji cewa duk da halin kunci da ake ciki a Najeriya, Hukumar Kwastam ta kama tirela makare da buhunnan wake 400.

Hukumar ta kama kayan ne a bakin iyakar Najeriya da ake shirin fita da su ba bisa ka’ida ba zuwa kasar ketare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel