Ministar Tinubu Ta Sake Samun Shirgegen Mukami a Kungiyar ECOWAS, Bola Ya Saka Albarka

Ministar Tinubu Ta Sake Samun Shirgegen Mukami a Kungiyar ECOWAS, Bola Ya Saka Albarka

  • Ministar jin kai da walwalar jama’a a Najeriya Dakta Betta Edu ta samu shirgegen mukami a kwamitin kungiyar ECOWAS
  • Edu ta samu mukamin ne bayan sahalewar shugaban kungiyar kuma shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a jiya Litinin
  • Betta Edu ita ce ministar jin kai da ke kula da bangaren walwalar jama’a da kuma rage radadin talauci musamman ga marasa karfi

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Ministar Jin kai da Walwalar Jama’a, Betta Edu ta samu babban mukamin a Majalisar Ministoci na kungiyar ECOWAS.

An nada Edu shuhgabar kwamitin Ministoci ta bangaren da ya shafi kare al’umma da walwalar jama'a na kungiyar, cewar Tribune.

Ministar Tinubu ta samu mukamin shugaban ministoci a kungiyar ECOWAS
Ministar ta samu mukamin ne da amincewar Tinubu. Hoto: Bola Tinubu, Betta Edu.
Asali: Facebook

Wane mukami ministar Tinubu, Edu ta samu?

Kara karanta wannan

Ku kara hakuri, Tinubu na da shirin ciyar da kasar nan gaba, shawarin minista ga 'yan Najeriya

Wannan na zuwa ne bayan sahalewar shugaban kungiyar kasashen ECOWAS kuma shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakta Edu ta kirayi kamfanoni masu zaman kansu da masu hannu da shuni da su ba da tasu gudunmawa a bangaren kare al’umma.

Yayin da ta ke jawabi a Banjul babban birnin Jamhuriyar Gambia a taron kwamitin Ministocin, Betta ta bukaci a kawo dauki ga al’umma musamman yaki da talauci.

Ta ce:

“Kare al’umma shi ne babban hakki na jama’a wanda bai zama taimako ba illa ya zama dole.
“Ba da kulawa na musamman ga al’umma da kare su ke kawo sauyi a lokacin rikici da rashin tabbas a cikin al’umma.”

Edu ta ce annubar Korona ya bayyana asalin bukatar kare al’umma musamman a yankin Nahiyar Afirka ta Yamma.

Yayin da ya ke jawabi, mataimakin shugaban kasar Gambia, Muhammad Jallow ya yabawa kasashen yankin Afirka ta Yamma da irin gudnmawar da su ke bayar wa.

Kara karanta wannan

Kano: Sakaci da dokar zabe ya jefa Gwamna Abba da NNPP cikon matsala, Kungiya ta bayyana

Ya ce gudunmawar ta taimaka wurin inganta rayuwar al’umma da toshe matsaloli da dama a yankin, cewar Vanguard.

Tinubu zai mika kasafin kudin 2024

A wani labarin, Shugaba Tinubu zai mika kasafin kudin shekarar 2024 a ranar Laraba 29 ga watan Nuwamba.

Wannan na zuwa bayan Majalisar Zartarwa ta amince da fiye da naira tiriliyan 27 a matsayin kasafin na shekarar mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel