APC
Hadimin shugaban kasa, Bola Tinubu na musamman, Daniel Bwala ya koka kan yadda wasu ke kwatanta Najeriya da kasar Ghana inda ya ce kasashe ba daya ba ne.
Gwamnatin jihar Benue ga ƙaryata rahoton da ake yaɗawa cewa tana nuna wariya ga wasu yan Majalisar dokoki masu goyon bayan Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.
Bayan gwamna ya rikice yayin gabatar da kasafin kudi a gaban Majalisa, shugaban APC a Edo, Jarrett Tenebe ya kare Gwamna Monday Okpebholo na jihar.
Chidi Odinkalu ya yi ikirarin cewa gwamnatin APC tana adawa da zanga-zanga, duk da sanin cewa ta samu nasarar hawa mulki ta hanyar zanga zanga ne a shekarar 2015.
Dan majalisar wakilai daga jihar Kano, Alhassan Ado Doguwa, ya fito ya nemi yafiya a wajen jam'iyyar APC reshen jihar Osun, kan wasu kalamai da ya yi.
Dan Majalisar Wakilai daga jihar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji ya karɓi dubban magoya bayan PDP da sauran jam'iyyun adawa a jihar zuwa jam'iyyar APC.
'Yan APC sun fara tabbatar da raguwar farin jinin jam'iyyar. Kusa a cikinta, Barista Ismael Ahmed ya ce akwai matsala a kasa. Ya bayyana cewa ba za su ci zabe ba.
Hadimin Atiku Abubakar ya tabbatar da cewa tsohon mataimakin shugaban kasa yana shiri da Peter Obi domin gyara kura-kuran da suka tafka a zaben 2023.
Jam’iyyar PDP a Najeriya ta ayyana kujerar yar Majalisar Tarayya kuma diya ga tsohon gwamnan Delta, Hon. Erhiatake Ibori-Suenu babu kowa bayan ta koma APC.
APC
Samu kari