Ana Murna Sauƙi Ya Fara Samuwa, Tinubu Ya Sake Tsoratar da 'Yan Najeriya, Ya Yi Jan Ido

Ana Murna Sauƙi Ya Fara Samuwa, Tinubu Ya Sake Tsoratar da 'Yan Najeriya, Ya Yi Jan Ido

  • Yayin da ake ci gaba da fama a Najeriya, shugaban kasa, Bola Tinubu ya ce ba zai gajiya wurin ɗaukar tsauraran matakai ba
  • Tinubu ya ce idan har ya san daukar kowane irin mataki zai kawo ci gaba a Najeriya to babu ruwansa da kunci da za a shiga na wani lokaci
  • Shugaban ya fadi haka a ranar Alhamis 25 ga watan Afrilu yayin ganawa da Fira Ministan Netherlands, Mark Rutte a birnin Hague

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Birnin Hague, Netherlands - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya ce zai ci gaba da ɗaukar matakai domin inganta rayuwar 'yan Najeriya.

Shugaban ya ce ko da kuwa 'yan kasar za su shiga halin matsi na dan lokaci amma dole zai dauki matakai masu muhimmanci.

Kara karanta wannan

"Shi ke haukata 'yan kasa", Malamin addini a Kaduna ya ja kunnen Tinubu kan halin kunci

Tinubu ya ce zai ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai domin ci gaban Najeriya
Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin inganta Najeriya ta kowane hali. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Yaushe Tinubu ya sha alwashin?

Tinubu ya bayyana haka ne yayin ganawa da Fira Ministan Netherlands, Mark Rutte a ranar Alhamis 25 ga watan Afrilu a birnin Hague, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kwarin guiwar 'yan kasar ne ya sa ya ke daukar matakai masu tsauri domin samun ingantacciyar rayuwa, cewar rahoton ThisDay.

"Mun shiga mummunan yanayi a kasar nan wanda yana daga mafi munin lokaci."
"Ba na tsoron abin da zai je ya dawo idan har nasan matakin da na dauka zai inganta rayuwar 'yan Najeriya a nan gaba."
"Naira na daga cikin kudi da ke taka rawa a fagen kasuwanci wanda hakan ya faru saboda tsauraran matakan da muka dauka dangane da haka."

- Bola Tinubu

Tinubu zai ci gaba da ɗaukar matakai

Shugaban ya ce a matsayinsu na shugabanni za su ci gaba da ɗaukar matakai domin kawo sauyi a kasar ba tare da jin tsoron komai ba.

Kara karanta wannan

An tafka babban rashi yayin da tsohon Sanata ya kwanta dama yana da shekaru 66

Ya ce naira ta na taka rawa a duniya inda ya ce hakan bai rasa nasaba da daukar tsauraran matakai da suka a ɓangaren tattalin arziki.

Fasto ya shawarci Tinubu kan halin kunci

A wani labarin, Fitaccen Fasto a jihar Kaduna, Rabaran Matthew Ndagoso ya bayyana irin matsalolin da 'yan Najeriya suka fada.

Faston ya ce halin kunci da rashin tsaro ya kara jefa 'yan ƙasar cikin rashin lafiyar kwakwalwa wanda dole a dauki matakai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel