Dakarun Sojoji Sun Ceto Ƙarin Mutane 15 Da Aka Sace a Jihar Zamfara

Dakarun Sojoji Sun Ceto Ƙarin Mutane 15 Da Aka Sace a Jihar Zamfara

  • Sojojin Najeriya sun kubutar da ƙarin mutane 15 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara ranar Litinin
  • Dakarun sojin rundunar Operation Hadarin Daji sun samu wannan nasara ne bayan sheƙe 'yan bindiga da dama a musayar wuta
  • Wannan na zuwa ne bayan an tabbatar da sojoji sun kubutar da ɗalibai 13 daga cikin waɗanda aka sace a Jami'ar Tarayya da ke Gusau

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Zamfara - Rundunar sojin Operation Hadarin Daji da ke aiki a Arewa maso Yammacin Najeriya ta ƙara samun gagarumar nasara kan 'yan bindiga a jihar Zamfara.

Dakarun sojin karkashin jagorancin kwamandan rundunar haɗin guiwa ta Operation Hadarin Daji, sun samu nasarar kubutar da ƙarin mutane 15 da aka sace a jihar.

Sojojin sun kubutar da ƙarin mutum 15 a Zamfara.
Dakarun Sojoji Sun Ceto Ƙarin Mutane 15 da Aka Sace a Jihar Zamfara Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Zagazola Makama, masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro, shi ne ya tabbatar da wannan nasara da sojojin suka samu a Zamfara a shafinsa na manhajar X.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Harbi Dalibai 3, Sun Sace Wata a Kwalejin Kimiyya a Wata Jihar Arewa

An tattaro cewa gwarazan jami'an sun kubutar da mutanen ne ranar Litinin, 25 ga watan Satumba, 2023 a ƙauyen Kayan Boggo, da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum a Zamfara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sojoji sun sheƙe wasu daga cikin 'yan bindigan

Zagazola ya fahimci cewa nan take bayan samun bayanan sirri, dakarun sojin suka durfafi hanyar da ake tunanin 'yan bindiga suna bi bayan sun kai hari, suka ɗana tarko.

Ya ce an yi artabu kuma jami'an tsaro sun halaka 'yan bindiga da dama, waɗanda ba a tantance yawansu ba, sauran kuma suka ari na kare zuwa cikin jeji.

"An yi musayar wuta kuma adadi mai yawa na 'yan bindigan sun sheƙa barzahu yayin da sauran suka arce cikin jeji bisa tilas suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su," in ji shi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Benue Ya Fusata Kan Sace Manyan Yan Siyasa a Jiharsa, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni

Majiyoyin soji sun ce an mika wadanda aka ceto ga hakimin Gwashi domin hada su da iyalansu.

Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan rahotanni sun tabbatar da sojoji sun ƙubutar da ƙarin ɗalibai mata 7 na jami'ar tarayya da ke Gusau.

Zamfara: Gwamna Lawal Ya Zargi Hukumomin FG da Tattaunawa da Yan Ta'adda

A wani rahoton kuma Gwamna Lawal ya faɗi mutanen da yake zargi daga FG sun fara tattaunawar sulhu da 'yan bindiga a jihar Zamfara.

Ya kuma jaddada matsayarsa cewa gwamnatinsa ba zata tattauna da 'yan bindiga ba domin a baya an yi amma babu sakamako mai kyau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel