Kannywood-Nollywood: Mista Ibu da Fitattun 'Yan Wasa 5 da Suka Mutu a Shekarar 2024

Kannywood-Nollywood: Mista Ibu da Fitattun 'Yan Wasa 5 da Suka Mutu a Shekarar 2024

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jarumai da dama a masana’antun fina finan Najeriya da suka hada da Kannywood (Arewa) da Nollywood (Kudu) suka riga mu gidan gaskiya a shekarar 2024.

Na baya bayan nan shi ne mutuwar jaruma Bintu ta shirin Dadin Kowa (a tashar Arewa 24) da kuma fitaccen jarumin barkwanci na kudu, Mista Ibu.

Kannywood-Nollywood: Mista Ibu da Bintu Dadin Kowa
Kannywood-Nollywood: Mista Ibu da Bintu Dadin Kowa da suka riga mu gidan gaskiya a 2024. Hoto: John Okafor (X), Bintu Dadinkowa (FB)
Asali: UGC

A wani bangare na karrama jaruman da suka rasu, ya zama wajibi mu yi waiwaye adon tafiya kan irin gagarumar gudunmawar da suka bayar a harkar fina finai a Najeriya.

Ga jerin jaruman Kannywood da Nollywood da suka mutu a shekarar 2024 zuwa yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Jam'iyyar APC a jihar Arewa ta yi wa Shugaba Tinubu wani babban albashir

Bintu Dadin Kowa ta rasu
Bintu Dadin Kowa tana cikin wadanda aka rasa a Kannywood/Nollywood. Hoto: Youtube/Arewa24, abbaelmustapha1/Instagram
Asali: UGC

1. Fatima Sa’id (Bintu Dadin Kowa)

Fatima Sa’id, wacce aka sanar da rasuwarta a ranar 11 ga Fabrairu, 2024, ta kasance shahararriyar jarumar Kannywood wadda ta fito a cikin shirin Dadin Kowa na Arewa24.

An haifi Bintu Dadin Kowa a shekarar 1999 kuma ta fito ne daga Gunduwawa, karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, Neptune Prime ta ruwaito.

Ta fara wasan kwaikwayo ne bayan ta fito a wani fim mai suna “BIL HAKKI”, daga baya kuma tauraruwarta ta fara haskawa bayan ta fito a shirin “Dadin Kowa”.

Mr Ibu ya mutu a ranar 2 ga watan Maris, 2024
Mr Ibu ya mutu a ranar 2 ga watan Maris, 2024 bayan fama da rashin lafiya. Hoto: John Okafor
Asali: Instagram

2. Mr. Ibu

A yammacin ranar Asabar 2 ga watan Maris 2023, shugaban kungiyar jaruman fina-finai ta Najeriya (AGN), Emeka Rollas ya tabbatar da mutuwar jarumin barkwanci, John Okafor, wanda aka fi sani da Mr Ibu.

A cikin Oktoba 2023, aka samu rahoton rashin lafiyar tsohon jarumin tare da neman taimakon kuɗi don yi masa magani, a watan Nuwamban 2023, aka yanke masa kafa daya.

Kara karanta wannan

Bayan mutuwar Mista Ibu, wata shahararriyar jarumar fina-finai a Najeriya ta tafka babban rashi

Mista Ibu ya fara fitowa a Nollywood a karshen shekarun 90s, kuma bai dade ba ya samu karbuwa bayan fitowa a fim din “Mr. Ibu,” da aka fitar a 2004.

Sisi Quadri ya mutu ne a ranar 1 ga watan Maris, 2024
Sisi Quadri ya mutu ne a ranar 1 ga watan Maris, 2024. Hoto: @sisiquadritv
Asali: Instagram

3. Sisi Quadri

Legit ma ta rahoto mutuwar jarumin Nollywood na Yarbawa, Tolani Quadri Oyebamiji, wanda aka fi sani da Sisi Quadri ya rasu ne a ranar 1 ga Maris, 2024 yana da shekaru 44.

Oyebamiji ya yi bikin cika shekaru 44 da haihuwa a ranar 25 ga Disamba, 2023.

Da take sanar da rasuwarsa, jarumar fina-finan Nollywood, Abiola Bayo ta rubuta a shafinta na Instagram, “Za a yi kewarka sosai, Sisi Quadri."

Ethel Ekpe ta mutu ne a ranar 7 ga watan Fabrairu, 2024.
Ethel Ekpe ta mutu ne a ranar 7 ga watan Fabrairu, 2024. Hoto: Ethel Ekpe.
Asali: Facebook

4. Ethel Ekpe

Fitacciyar ‘yar wasan kwaikwayo, Ethel Ekpe, wadda ta taka rawa sosai a masana'antar Nollywood ta rasu ne sakamakon cutar daji a ranar Laraba, 7 ga Fabrairu, 2024 a jihar Legas.

Legit ta tattaro cewa Ekpe, wadda ta shahara wajen taka rawar ‘Segi’ a shirin gidan talabijin na NTA, ‘Basi and Company’, ta rasu ne bayan fama da cutar daji.

Kara karanta wannan

'Yar bautar kasa ta tsinci wayar iPhone 13 Pro Max da ta kai miliyan 1.3, ta mayarwa mai ita

Olofaina Ina ya mutu a ranar 4 ga watan Fabrairu, 2024.
Olofaina Ina ya mutu a ranar 4 ga watan Fabrairu, 2024. Hoto: @saidibalogun
Asali: Instagram

5. Olofa Ina

Shahararren jarumin yarbawa Deji Aderemi wanda aka fi sani da Olofa Ina ya rasu ne a ranar Alhamis 4 ga watan Junairu 2024. Ya rasu yana da shekaru 73 a duniya.

Vanguard ta ruwaito cewa jarumin ya rasu ne sakamakon cutar daji a jihar Legas.

Jaruman Kannywood 5 da suka rasu a 2023

Tun da fari, Legit Hausa ta fara kawo maku rahoton mutuwar wasu manyan jarumai 5 na masana'antar Kannywood a shekarar 2023.

A waccan shekarar, Masana'antar Kannywood ta girgiza matuka da mutuwar jarumin barkwanci Kamal Aboki, sai dai rasuwar darakta Aminu S. Bono ta tsayar da komai a masana'antar na dogon lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel