Kungiya Ta Yi Kira Ga Abba Ya Dawo da Tsarin Masarauta 1 a Kano, a Rushe Rano, Gaya, Bichi da Karaye

Kungiya Ta Yi Kira Ga Abba Ya Dawo da Tsarin Masarauta 1 a Kano, a Rushe Rano, Gaya, Bichi da Karaye

  • Kungiyar KACDA, wacce ke rajin kare martabar al'adun jihar Kano, ta yi kira ga gwamnatin jihar, da ya rushe tsarin masarautu biyar
  • Kungiyar ta nemi da a dawo da tsarin sarki ɗaya tilo a jihar domin dawo da martaba da kwarjinin masarautar Kano a idon duniya
  • Shugaban kungiyar, A.G. Shittu ya koka kan yadda aka samu rarrabuwar kawunan al'umma da lalacewar al'adu saboda raba masarautun

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Kungiyar kare martabar al'adun gargajiya ta Kano (KACDA) ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta rushe tsarin masarautu biyar a jihar.

Kungiyar wacce ta aika wa Gwamna Abba Kabir Yusuf wata wasiƙa kan wannan bukatar ta ce rabuwar masarautun ta rage daraja da martabar babbar masarautar Kano.

Kara karanta wannan

An karrama sojoji 8 da suka ƙi karbar cin hancin naira miliyan 1.5 daga hannun ɓarayin shanu

An yi kira ga Abba ya rusa tsarin masarautu biyar a Kano
Kungiyar ta yi nuni da cewa tsarin masarautu biyar ya rage kwarjinin masarautar Kano. Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Wasikar wacce ke dauke da sa hannun shugaban kunyar KACDA na jihar, A.G. Shittu na magana ne akan masarautun Rano, Gaya, Bichi da Karaye da aƙa kirkira a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A.G. Shittu ya ce raba masarautar da aka yi gida biyar ya jawo rarrabuwar kawuna da lalacewar al'adun dauri wadanda aka san masarautar Kano da su.

An rage wa masarautar Kano kwarjini a idon duniya

A zantawarsa da Legit Hausa, Shittu ya ce:

"Misalin hawan daba da ake yi a bikin Sallah, kafin rabuwar masarautun, dukkan kananan hukumomi 44 na haduwa a masarauta daya ne, amma yanzu an raba kawunan mutane..
"Daraja da martabar masarautar Kano ta yi ƙasa, maimakon sarki guda ɗaya mai cikakken iko, yanzu sarakuna biyar ne, don haka ita uwar masarautar an rage mata kwarjini a idon duniya"

KACDA ta nemi a rushe masarautun hudu

Kara karanta wannan

Yan sanda sun dakatar da zanga-zangar NLC a Borno a kan wani dalili 1 tak

Shugaban kungiyar ya ce sun aika wa gwamnan wasikar don ankarar da shi illar da take tattare da rabuwar masarautun da kuma ba shi shawarar hanyar dawo da martabar Kano.

Ya ce:

"Ya zama wajibi gwamnatin Kano da majalisar jihar Kano su yi fatali da waccan doka da ta kafa masarautun Rano, Gaya, Bichi da Karaye ma damar ana son dawo da martabar masarautar Kano.
"Dawo da tsarin sarki ɗaya a Kano shi ne kawai hanyar dawo da hadin kai, dorewar al'adu da kuma ci gaba da kasancewar masarautar Kano ginshikin masarautun Najeriya."

Wa za a nada sabon Sarkin Kano?

Ko da aka tambaye shi akan wanda ya ke ganin zai zama sabon sarki idan an hade masarautun waje daya, Shittu ya ce:

"Dukkannin wadanda suke da sha'awar zama kan kujerar, za su aika da bukatar hakan, muna da yakinin gwamnati za ta zabi wanda ya fi cancanta ya zama Sarki.

Kara karanta wannan

Hotunan yadda Kanawa suka karade titunan Kano a zanga-zangar kin jinin tsadar rayuwa

"Kamar tsohon Sarki Sanusi Lamido Sanusi, wanda mutane ke kira akan a mayar da shi sarki, idan har gwamnati ta duba ta ga shi ne ya fi cancanta, sai a dawo da shi kan kujerarsa."

Masarautar Kano: Kungiyoyi sun nemi a dawo da Sanusi II

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa mutane da dama na ta kiraye-kiraye ga majalisar jihar Kano da ta dawo da Sanusi Lamido Sanusi matsayin Sarkin Kano.

A baya-bayan nan wata magoya bayan NNPP a Kano ta yi kira ga majalisar da ta rushe dokar ta sauke Sanusi tare da dawo da shi kan karagar mulkin masarautar jihar

Asali: Legit.ng

Online view pixel