Dalilin da yasa Ganduje ya ke son kawo sauyi a tsarin masarautun Kano
- Alhaji Tijjani Mailafiya, mai bai wa gwamna Ganduje shawara a kan harkar masarautu, ya amsa wasu tambayoyi
- A cewarsa, ba a raba masarautar Kano don a cuzguna ko a muzguna wa Sunusi Lamido Sunusi ba, an yi ne don taimakon al'umma
- A cewarsa, musamman yadda harkar tsaro ta lalace, wajibi ne gwamnati ta janyo mutane a jiki, rabawar tana da fa'ida
Alhaji Tijjani Mailafiya Sanka ne mai bai wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano shawarwari a kan al'amuran masarutu, jaridar Daily Trust ta wallafa hakan.
A wata tattaunawa da aka yi da shi, ya yi magana a kan abinda ya sanya gwamnan komawa majalisar jiha don gyara sababbin dokokin masarautar.
Da farko dai masu korafi a kan rarraba masarautar kuma suka kai kotu za su jira har bayan annobar COVID-19. Saboda annobar ta hana mutane da yawa su taru wuri guda, don haka sai komai ya daidaita za a cigaba da shari'ar.
KU KARANTA: Sojin Najeriya sun fatattaki 'yan bindiga a hanyar Kaduna zuwa Abuja, sun ragargaza wasu
Gwamnatin jihar Kano da masarautar sun yi nisa wurin shirya yadda za a yi shagulgulan nadin sarautar.
Sarakunan 3 dake shirin lokacin nadin sun hada da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero; Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero da Sarkin Rano, Alhaji Kabir Muhammad Inuwa, wanda aka nada bayan mutuwar wanda ya gaji sarautar daga gareshi.
Yanzu haka ana cigaba da shirye-shirye, sannan kwanan nan za a sanar da lokacin nadin da izinin Allah.
KU KARANTA: Soji sun kashe mayakan Boko Haram 23, sun cafke kwararren mai hada bam
Da aka tambayeshi dalilin da tun bayan samar da masarautun, Gwamna Ganduje yayi ta bukatar 'yan majalisar jiharsa su amince da gyara dokoki, kusan sau 3.
Cewa yayi Gwamnan yana yin hakan ne don jihar ta amfana. Gwamnati tana kokarin ganin ta samar da dokokin da za su taimaki al'umma.
A cewarsa, mutane da dama suna ganin kamar an raba masarautar ne don a bata wa Sunusi Lamido rai, amma ba haka bane. An yi ne don taimakon jama'a da janyo su a jiki, musamman yadda harkokin tsaro suka tabarbare.
A wani labari na daban, hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wani dan sanda Basiru a wuraren Rumawa da ke karamar hukumar Ungogo a kan laifin lalata, Vanguard ta wallafa.
Kamar yadda hukumar tace, an kama har da Basiru abokin Jamilu a wani daki da ke wuraren Rumawa, inda suka boye suna aikata alfashar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng