Raba masarautar Kano, raba jama’a Kano ne har abada - Gumi (bidiyo)
Jama’a na ci gaba da tofa albarkacin bakunansu akan rarraba masarautar Kano zuwa yanka biyar da gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje tayi.
Babban malamin nan na addinin Musulunci, Sheikh Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi tsokaci akan lamarin.
A cewar malamin, wannan yunkuri zai rarraba kan Kanawa ne, kuma shi addinin Musulunci baya son ayi ta rabuwa, haduwa yake so.
Ya kara da cewa a yanzu maimakon aji Magana daya ya fito daga Kano sai aji maganganu biyar sun fito, ta haka ne makiyan addini za su samu su shigo.
Gumi yace idan har ana son a samu nasara sai an samu shugaba wanda zai iya hada kan al’umma, ya kira kowa, a lallashi kowa sannan ya nuna ma mutane alkibla, shi kadai ne sai samu nasara.
Ga kalamun nashi: “Yanzu na ji ana son a tsatsage kasar Kano, shi Musulunci na son haduwa, ba wai rabuwa ba, A wannan rabuwar wani na jin dadin zai zamo sarki wannan ba shine lafiya ba. Yanzu maimakon magana daya ya fito daga Kano sai a ji magana biyar ta fito, kaga an raba kan Kanawa har abada, kuma kai kanka da ka raba su, nan gaba za ka fito kana son ka hada su amma baka iyawa.
“Haka nan za a ta rarrabawu shikenan sai makiyan addini su samu hanya da za su samu nasara a kanmu.
KU KARANTA KUMA: Kowa ya samu rana yayi shanya: Ganduje ya nada sabon Alkalin Alkalai a jahar Kano
“Abunda ya kawo wannan duk saboda ahlul hak na Kano basu da magana a mulki. Na ji wani na kuka yana ina manyanmu, ina yan kasuwarmu, ina dattijanmu, ina malaman mu, su kansu kawunansu a rarrabe yake, idan ana son a samu nasara sai an samu shugaba wanda zai iya hada kan al’umma, ya kira kowa, a lallashi kowa sannan ya nuna ma mutane alkibla, shi kadai ne sai samu nasara.”
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu. Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Read more: https://hausa.legit.ng/1237662-yanzu-yanzu-sanusi-ya-samu-mukami-a-majalisar-dinkin-duniya-kwana-daya-bayan-kacaccala-masarautarsa.html
Asali: Legit.ng