"Sabon Gwamna, Sabon Sarki": An Fara Kira a Mayar Da Sanusi Sarautar Kano Bayan Nasarar Abba a Kotu

"Sabon Gwamna, Sabon Sarki": An Fara Kira a Mayar Da Sanusi Sarautar Kano Bayan Nasarar Abba a Kotu

  • Da alamu kiraye-kirayen mayar da tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi sun fara tasiri a jihar Kano bayan nasarar Abba Kabir
  • Magoya bayan gwamnan sun bukaci a sake duba dokar da ta tabbatar da masarautun jihar don dawo da tsohon Sarkin kan kujerarshi
  • Wannan na zuwa ne bayan tube tsohon Sarkin daga kujerar wanda Abdullahi Ganduje ya yi a shekarar 2020

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Tun bayan nasarar Gwamna Abba Kabir a Kotun Koli, aka fara kiraye-kirayen dawo da tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi.

Magoya bayan gwamnan sun bukaci a sake duba dokar da ta tabbatar da masarautun jihar don dawo da Sunusi Lamido kan kujerarshi.

Kara karanta wannan

Tsageru sun farmaki motar kamfen mataimakin gwamnan PDP, sun tafka mummunar ɓarna

Akwai alamu tsohon Sarkin Kano ya dawo kujerarshi bayan kiraye-kiraye
An tube tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi a 2020. Hoto: Sunusi Lamido, Abba Kabir.
Asali: Original

Mene magoya bayan Abba Kabir ke cewa kan Sunusi?

Idan ba a mantaba, tsohon gwamnan jihar, Abdulllahi Ganduje shi ya tube Sunusi a kujerar Sarkin Kano a shekarar 2020.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai magoya bayan gwamnan yayin da suka fito tarbar Abba Kabir a Kano sun yi ta shelar cewa "Sabon Gwamna, sabon Sarki", cewar Leadership.

Wannan kira har ila yau, ta karade kafofin sadarwa don ganin an dawo da tsohon sarkin, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Mene Abba Kabir ya ce kan lamarin a baya?

A ranar 29 ga watan Mayu bayan Abba Kabir ya karbi rantsuwa ya yi magana kan matakin dawo da Sunusi Lamido Sunusi kan kujerar.

Abba ya ce bai yanke wani hukunci ko wata shawara ba game da masarautun da tsohon gwamnan jihar ya kirkiro.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ya warware abin da Ganduje ya so a shiryawa Kano a Kotun Koli Inji Abba

Martanin na shi na zuwa ne bayan jita-jitar cewa da zarar ya hau karagar mulki zai rusa sabbin masarautun a jihar.

Wata majiya ta tabbatar da cewa lamarin na kara girma wanda ake tunanin yin doka don turawa Majalisar jihar kan sabunta dokar masarautun.

NNPP ta yi martani kan hukuncin kotu a Kano

A wani labarin, jami'yyar NNPP ta yi martani bayan nasarar Gwamna Abba Kabir na jihar Kano a Kotun Koli.

Jami'yyar ta ce nasarar ta kunyata 'yan sha miyar siyasa wadanda ke kulla munafurci don biyan bukatar kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel