Ta faru ta kare: Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kafa masarautu hudu a jihar Kano

Ta faru ta kare: Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kafa masarautu hudu a jihar Kano

- A yanzu haka dai majalisar dokokin jihar Kano ta ce ta gama shiri tsaf domin mikawa gwamnan jihar dokar kafa sababbin masarautu guda hudu a fadin jihar

- Haka shima gwamnan jihar a yau da safen nan ya yi alkawarin cewa a shirye yake domin ya sanya hannu akan dokar da za ta ba da damar kafa masarautu guda hudu a jihar

Majalisar dokokin jihar Kano karkashin jagorancin kakakin majalisar Rt. Hon Alhassan Rurum ta amince da kafa sababbin masarautu guda hudu a fadin jihar Kano.

"Ba a samu wadanda suka nuna rashin amincewar su ba a dakin majalisar. Sai dai akwai wadanda suka dinga fita daga majalisar wadanda alamu ke nuna cewa ba su ji dadin dokar ba," wani dan majalisar wanda ya bukaci a boye sunansa, ya bayyanawa manema labarai cewa.

Ta faru ta kare: Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kafa masarautu hudu a jihar Kano
Ta faru ta kare: Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kafa masarautu hudu a jihar Kano
Asali: Facebook

"Gwamnan jihar ya na so ya rage darajar sarkin Kano, Sanusi Lamido a idon duniya, shi ne ya sanya ya ke so ya kirkiri masarautun guda hudu ya sanya su a matsayi daya da sarkin Kanon."

Garuruwan da dokar ta yadda su yi sarautar sun hada da Masarautar Kano, Masarautar Rano, Masarautar Gaya, Masarautar Karaye da kuma Masarautar Bichi.

KU KARANTA: Cuwa-cuwa wajen bayar da kwangila ne ummul aba'isin rashin kammala ayyuka

A yanzu haka dai ana shirin mika dokar wajen Mai Girma Gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje domin ya rattaba hannu akan dokar wacce za ta share hanya akan nadin sababbin sarakunan Kanon na yanka.

A yau dinnan, gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, ya yi alkawarin cewa zai sanya hannu akan dokar da an gabatar da ita gareshi.

Ganduje ya bayyana hakan yau Larabar nan a wata hira da yayi da manema labarai a gidan gwamnatin jihar Kano.

"Mun samu labarin dokar da aka aikawa gidan gwamnatin jihar Kano, inda aka bukaci ta sanya hannu a dokar kafa sababbin masarautun yanka guda hudu a jihar nan.

"Muna fatan wadanda suka bukaci hakan sun bukaci hakan da zuciya daya ne. Kuma muna fatan sunyi hakan da niyyar samun cigaba ga jihar Kano baki daya," in ji Ganduje.

A satin da ya gabata ne dai gwamnatin jihar Kanon a karkashin gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta fara shawara akan yadda za ta kafa doka wacce za ta bata damar kafa masarautun yanka guda hudu a fadin jihar.

Hakan bai yiwa mutane da yawa dadi ba musamman ma Sarkin Kano Muhammad Sanusi na II, wanda shi ne za a yiwa kishiya.

To sai dai ba a san ainahin wainar da ake toyawa ba a cikin fadar jihar Kanon, domin kuwa tun lokacin da aka fara maganar kafa masarautun jihar har yanzu fadar jihar ba ta ce komai akan hakan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel