Muhimman Matakai 6 da Aka Dauka da Tinubu Ya Zauna da Gwamnoni a Aso Villa

Muhimman Matakai 6 da Aka Dauka da Tinubu Ya Zauna da Gwamnoni a Aso Villa

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi zama da gwamnoni a kan halin tsadar rayuwar da mutane suka shiga a Najeriya
  • Gwamnonin jihohi da yawa sun halarci taron da aka yi a fadar Aso Rock tare da Kashim Shettima a garin Abuja
  • Shugaban Najeriyan ya yi kira na musamman ga gwamnoni domin a magance tsadar farashi da wahalar abinci

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya hadu da gwamnonin jihohin Najeriya a game da halin kuncin rayuwar da al’umma su ka shiga.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya na cikin wadanda aka yi zaman da su kamar yadda Punch ta kawo rahoto.

Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya hadu da Gwamnoni a Abuja Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Haduwar Tinubu da Gwamnoni a Aso Rock

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya ba jami'an tsaro umarnin cafke masu boye kayan abinci

Baya ga gwamnoni, Nyesom Wike yana wajen taron a matsayinsa na Ministan Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi zaman ne a fadar shugaban kasa na Aso Rock Villa da ke Abuja da korafi ya fara yawa kan tsadar rayuwa da wahalar abinci.

Temitope Ajayi ya fitar da gajeren jawabi a shafinsa na X bayan zaman da aka yi dazu.

Mai taimakawa shugaban kasar ya bayyana jeringiyar matakan da aka cin ma bayan wannan zama na musamman da aka yi dazu.

Jawabin ya samu sa hannun mai taimakawa shugaba Bola Tinubu wajen yada labarai da kuma dabaru watau Mista Bayo Onanuga.

Matsayar zaman Tinubu v Gwamnoni

1. Inganta tsaro

Za a bukaci daukar karin ‘yan sanda domin shawo kan matsalar tsaro wanda hakan ya kawo matsala wajen noman abinci a kasar.

Za a hada-kai da ‘yan majalisar tarayya domin kafa ‘yan sanda a matakin jihohi a madadin jami’an sa-kai da gwamnoni su ke kirkira.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu da gwamnoni sun fara shirin ɗaukar mataki 1 da zai magance matsalar tsaro a Najeriya

2. Tsadar abinci

Bola Tinubu ya soki yadda ake boye abinci kuma ya ce a maida hankali ga noma, ya yi gargadi a kan bude iyakoki domin kawo abinci.

3. Boye abinci

Shugaban kasa ya ba gwamnoni shawara suyi koyi da Abba Kabir Yusuf, kuma zai kafa kwamiti da zai yi maganin masu boye kayan abinci.

4. Inganta noma

Jawabin ya ce shugaba Bola Tinubu ya kuma bukaci gwamnoni su maida hankali a sha’anin kiwo musamman kiwon dabbobi da kifi a jihohi.

5. Albashi

Ajayi ya shaidawa Najeriya an nemi gwamnoni su rika biyan hakkokin ma’aikata kan kari, musamman tun da kudin da ake samu a FAAC ya karu.

6. Dabarun tattalin arziki

A karshe an yi kira ga gwamnatocin jihohi su fito da dabarun samun kudi, kuma a tabbata matasa sun samu abin yi, a daina zaman banza.

Bola Tinubu zai fuskanci kalubale

Baya ga wahalar rayuwa, kungiyoyin ‘yan kwadago su na barazanar shiga yajin-aiki saboda zargin gwamnati da saba alkawarin da ta dauka.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnan APC ya fara raba kayan tallafi na biliyan 5 ga mabukata

Tsofaffin ma’aikata sun shirya za su yi zanga-zanga tsirara saboda rashin biyansu fansho wanda hakan ya hurowa gwamnatin kasar wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel