Tsadar Rayuwa: Tinubu Ya Ba Jami’an Tsaro Umarnin Cafke Masu Boye Kayan Abinci

Tsadar Rayuwa: Tinubu Ya Ba Jami’an Tsaro Umarnin Cafke Masu Boye Kayan Abinci

  • Gwamnatin tarayya ta ba jami'an tsaro umarnin hada kai da gwamnoni wajen kama masu boye kayan abinci a fadin Najeriya
  • Wannan umarnin ya biyo bayan yadda abinci ya yi karanci tare da yin tsada a kasar, lamarin ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali
  • Sai dai kuma, wasu 'yan kasuwa a zantawarsa da Legit Hausa, sun yi fargabar cewa za a yi amfani da hakan wajen zaluntar 'yan kasuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A ranar Alhamis ne shugaban kasa Bola Tinubu ya umurci hukumomin tsaro da su kama duk wanda aka same shi da laifin tara kayan abinci suna boyewa a Najeriya.

A cewar rahoton Leadership, wannan dai ya biyo bayan ganawar da shugaban kasar ya yi da gwamnonin jihohi a Abuja kan tsadar abinci da kasar ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Tsadar abinci: Gwamnati ta rufe wani babban kanti a Abuja, an samu cikakken bayani

Tinubu ya ba jami’an tsaro umarnin kama masu boye kayan abinci.
Tinubu ya ba jami’an tsaro umarnin kama masu boye kayan abinci. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Tsadar kayan abinci ta haifar da zanga-zanga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zangar ta barke a jihar Neja a makon da ya gabata don nuna adawa da tsadar kayan abinci a kasar wanda wasu da dama kuma ke dangantawa da boye kayan abinci da wasu ke yi.

A jihar Kano, sai da gwamnati ta kwace wasu rumbunan ajiya guda 10 da aka ce an boye kayan abinci a jihar.

Da yake jawabi kan wannan kalubalen, ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya ce Tinubu ya umurci shugabannin tsaro da su hada kai da gwamnonin jihohi, Daily Trust ta ruwaito.

Dalilin da ya sa za a fara kama masu boye kayan abinci

Bayan ganawar da shugaba Tinubu yayi da gwamnonin jihohi a ranar Alhamis, ministan ya ce:

“An ba mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, sufeto janar na ‘yan sanda; da daraktan hukumar DSS umarni su hada kai da gwamnoni don magance matsalar masu boye abinci.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya ki karbar shawarar bude iyakoki da kayyade farashin abinci

“A wannan lokaci ne al’ummar kasar ke bukatar a fito wa jama’a abinci domin mu iya daidaita farashi da kuma wadatar da abincin a gidajen yawancin ‘yan Najeriya."

A batun kan gwamnati za ta shigo da abinci domin saukaka tsadar kayan abinci, Idris ya ce hakan ba zai zama dole ba domin kasar na da damar ciyar da kanta.

Abun da 'yan kasuwa ke cewa game da wannan mataki

A zantawar Legit Hausa da wasu 'yan kasuwa, sun nuna fargabar cewa jami'an gwamnati za su iya amfani da wannan damar wajen balle shagunan 'yan kasuwa ba tare da wani dalili ba.

Alhaji Garba Mai Treda daga jihar Katsina ya ce akwai 'yan kasuwar da su ne ke noma kayan da suke siyarwa, wasu kuma sukan sayo kayan da yawa, wanda bai kamata ace boye suka yi ba.

"Bari na baka misali, kamar irin su Mangal a Katsina ko Jargaba a Funtua, sukan noma kayan abincin da zai iya shekara uku a ajiye, kuma duk shekara sai sun kara yin wani noman.

Kara karanta wannan

Kasar Girka ta kuduri aniyar halatta auren jinsi, da daukar rainon yara

"Akwai 'yan kasuwar da ana iya sauke masu tirela 10 zuwa 50 na shinkafa, sukari, da sauran kayan abinci, shin don sun adana shi sai ace sun yi laifi har a nemi a kwace masu kaya?"

A cewar Alhaji Mai Tireda.

Ya nemi gwamnati da ta samar da hukumar kayyade farashin kayayyakin abinci, mai makon "bude kofar zaluntar 'yan kasuwa."

Shi kuwa Salmanu Ma'aji, daga kasuwar Muda Lawan Bauchi, ya yi nuni da cewa, matakin gwamnati na kama masu boye kayan abinci zai karya farashin kayan a kasuwanni

Ya bayyana cewa, a yanzu da kayan abinci ke tsada, idan 'yan kasuwar suka zabi fito da su don kar a kama su, dole su sauke farashi don ganin sun sayar da su da wuri.

Yan kasuwar Dawanau sun karya farashin kayan abinci a Kano

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa kungiyar 'yan kasuwar Dawanau da ke jihar Kano, sun karya farashin kayan hatsi.

Sakamakon yadda farashin kayan suka hauhawa a baya, wannan ya jawo karancin masu sayen kayan, a cewar shugaban kungiyar, Alhaji Isah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Tags:
Online view pixel