Jerin Gwamnonin da Suka Halarci Ganawa da Shugaba Tinubu Kan Tsadar Abinci da Muhimmin Abu 1

Jerin Gwamnonin da Suka Halarci Ganawa da Shugaba Tinubu Kan Tsadar Abinci da Muhimmin Abu 1

  • Bola Tinubu ya yi ganawar gaggawa da gwamnonin jihohi kan muhimman batutuwan da suka taso musamman tsaro da tsadar rayuwa
  • Legit Hausa ta tattaro muku gwamnonin da suka samu damar halartar wannan zama da aka yi a fadar shugaban ƙasa ranar Alhamis
  • Wannan taro dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan kungiyar gwamnonin PDP ta kwatanta halin da Najeriya ta shiga da na ƙasar Venezuela

FCT Abuja - A ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnonin jihohi kan tsadar rayuwa da taɓarɓarewar tsaro.

Ofishin mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin midiya ya tabbatar da haka a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

Gwamnoni sun gana da Tinubu.
Jerin Gwamnonin da Suka Halarci Zama da Tinubu Kan Tsadar Rayuwa da Tsaro Hoto: Dolusegun16
Asali: Twitter

Taron wanda aka fara da misalin karfe 11:30 na safe ya samu halartar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da sufetan yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun.

Kara karanta wannan

Muhimman matakai 6 da aka dauka da Tinubu ya zauna da Gwamnoni a Aso Villa

Shugaba Tinubu ya kira wannan taro ne saboda halin matsin tattalin arzikin da aka shiga da matsalar tsaron da ke ƙara ƙamari a sassan ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ganawa ta gaggawa na zuwa ne kwanaki kalilan bayan gwamnonin jam'iyyar PDP sun kwatanta halin da Najeriya ta shiga da na ƙasar Venezuela.

Jerin gwamnonin da aka tabbatar sun halarci taron

Legit Hausa ta tattaro muku jerin sunayen gwamnonin jihohin da aka hanga sun shiga wannan taro da nufin lalubo mafita ga tsadar rayuwa da sha'anin tsaro. Ga su kamar haka:

1. Mai Mala Buni na Yobe

2. Charles Soludo na Anambra

3. Fasto Umo Eno na Akwa Ibom

4. Alex Otti na Abia

5. Celeb Mutfwang na Filato

6. Malam Uba Sani na Kaduna

7. Ahmed Aliyu na Sokoto

8. Mohammed Umar Bago na Neja

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu da gwamnoni sun fara shirin ɗaukar mataki 1 da zai magance matsalar tsaro a Najeriya

9. Agbu Kefas na Taraba

10. Ahmadu Fintiri na Adamawa

11. Sanata Bassey Otu na Kuros Riba

12. Dapo Abiodun na Ogun

13. Peter Mbah na Enugu

14. Biodun Oyebanji na Ekiti

15. Sheriff Oborevwori na Delta

16. Farfesa Babagana Umaru Zulum na Borno

17. Babajide Sanwo-Olu na Legas

18. AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara

19. Abdullahi Sule na Nasarawa

20. Godwin Obaseki na Edo.

FG da gwamnoni sun fara tattauna batun ƴan sandan jihohi

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu da gwamnoni sun fara cimma matsaya kan batun kafa yan sandan jihohi da nufin kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka ga masu ɗauko rahoto a fadar shugaban kasa ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262