Tashin Hankali Yayin da Wani Dan Sanda Ya Kashe Abokin Aikinsa a Rivers, Shi Ma Ya Bindige Kansa

Tashin Hankali Yayin da Wani Dan Sanda Ya Kashe Abokin Aikinsa a Rivers, Shi Ma Ya Bindige Kansa

  • Mutanen garin Nyogor-Lueke da ke jihar Rvers sun shiga tashin hankali yayin da wani dan sanda ya kashe kansa bayan kashe abokinsa
  • Sufeto Nelson Abuante ya aikata danyen aikin ne a wani aiki da ya fita tare da Sufeto Monday Gbramana, aikin da aka dawo da gawarwarkin su
  • Rahotanni sun bayyana cewa Sufeto Abuante ya harbi abokin aikinsa Sufeto Gbramana bisa kuskure, amma ganin abin da ya aikata, shi ma ya dau ransa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Rivers - Wani Sufeto a rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ya kashe kansa bayan da aka ce ya harbe abokin aikinsa Monday Gbaramana har lahira.

Rahotanni sun bayyana cewa dan sandan mai suna Sufeto Nelson Abuante ya harbe abokin aikinsa a ranar Lahadi a Nyogor-Lueku da ke karamar hukumar Khana a jihar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai sabon farmaki kauyen Sokoto, sun yi mummunar barna

Sufeton 'yan sanda ya kashe kansa bayan kashe abokin aikinsa a Rivers
Sufeto a rundunar ‘yan sandan Rivers ya kashe kansa bayan da aka ce ya harbe abokin aikinsa har lahira. Hoto: @RiversPoliceNG
Asali: Twitter

Yadda abin ya faru har ta kai ga mutuwar 'yan sandan

Dukkanin su suna aiki da sashin Taabaa na rundunar kuma sun je kama wani mai laifi ne lokacin da wannan mummunan abu ya faru, rahoton jaridar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai matsalar ta fara ne lokacin da wanda ake zargin Akere Akpobari ya bijirewa yunkurin kama shi. Ana tsaka da hakan ne Sufeto Abuante ya yi kuskuren harbin Sufeto Gbaramana.

Gbaramana ya samu raunuka kuma nan take aka garzaya da shi asibiti. Sai dai lamarin ya munana bayan da fetur ya kare a motar da ta dauke su, jinkirin da ya yi ajalin Gbaramana.

Ganin abin da ya faru sai Abuante ya juya bindigar ya kashe kansa, Channels TV ta ruwaito.

Dangane da lamarin, kakakin ‘yan sanda a Rivers Grace Iringe-Koko ta ce:

Kara karanta wannan

Tsaka mai wuya: Sama da 'yan Najeriya 1,000 aka damfara da sunan sama masu aiki a Burtaniya

“An ajiye gawarwakin biyu a dakin ajiyar gawarwaki yayin da ake ci gaba da bincike”.

Yan sanda sun kama dalibin jami'ar ATBU Bauchi da bindiga

A wani labarin, rundunar 'yan sanda ta cafke wani dalibin jami'ar ATBU Bauchi mai suna Atim Emmanuel kan mallakar bindiga da harsashi.

Mai magana da yawun rundunar, SP Ahmed Mohammed Wakil ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce an kama dalibin a ranar 11 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel