Kare ya ceto wata mage da suka jima suna abota tare daga wani gida da gobara ta kama

Kare ya ceto wata mage da suka jima suna abota tare daga wani gida da gobara ta kama

Wannan wani labari ne mai shiga zuciya sosai, labarin da ya faru a kasar Ukraine, kwanaki kadan da suka gabata. Amma duk da haka muna ganin yana da matukar amfani mu sanar da mutane

Wata wuta da ta kama a wani kamfani dake birnin Donetsk ita ce babbar dalilin bayar da labarin. Wuta ganga-ganga ta kama, hayaki ya cika ko ina a sararin samaniya, inda mutanen da suke da nisan kilomita 5 da kamfanin suma hayakin ya dame su.

Mutanen yankin da lamarin ya faru tilas ta sanya suka tashi daga yankin baki daya, inda kowa yake daukar iya abinda zai iya dauka yana fita da gudu. Sai dai kuma wani kare yaki fita daga wajen, yayin da kowa yake gudu shi kuma komawa ciki yake yi.

Kare ya ceto wata mage da suka jima suna abota tare daga wani gida da gobara ta kama
Kare ya ceto wata mage da suka jima suna abota tare daga wani gida da gobara ta kama
Asali: Facebook

Mutumin da ya mallaki karen abin ya bashi mamaki da tsoro, sai kawai ya tsaya yana kallon ikon Allah, saboda ba zai iya shiga cikin kamfanin domin ceto karen na shi ba, saboda wutar na kara ruruwa a kowanne lokaci.

KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Sama da mutane 24 ne suka rasu sanadiyyar hadarin mota da ya faru a jihar Jigawa

Mutumin addu’ar da yake a wannan lokacin shine ya samu karen shi ya fito lafiya. Yana tsaye can sai ya gano karen yana fitowa daga cikin gidan. Amma kuma ba shi daya bane, a bakin shi yana rike da wata karamar mage wacce suke zaune tare da ita.

Abokanai ne sosai, suna zaune tare a kowanne lokaci. A lokacin da wutar ta kama babban burin shi a lokacin shine ya ceto rayuwar kawarshi. Mai karen yayi matukar mamaki akan abinda wannan kare yayi.

Saboda magen karama ce ba za ta iya fitowa daga cikin gidan ba, Allah yasa abokinta ya tuna da ita yaje ya ceto rayuwarta. Mutanen yankin da suka ji wannan labari sun jinjinawa karen sosai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel