Tsadar Rayuwa: Ta Yiwu Tinubu Ya Rufe Iyakar Najeriya Kan Karancin Abinci, Ya Fadi Sauran Hanyoyi

Tsadar Rayuwa: Ta Yiwu Tinubu Ya Rufe Iyakar Najeriya Kan Karancin Abinci, Ya Fadi Sauran Hanyoyi

  • Minsitan Noma a Najeriya, Abubakar Kyari ya ce babu wani abin da ya dace sai rufe iyaka idan har komai ba dawo dai-dai ba
  • Kyari ya ce daga cikin matsalolin da ake fuskanta yanzu na karancin abinci har da rashin tsari a gwamnatin Buhari kan noma
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani malami kuma masanin tattalin arziki kan wannan mataki na Gwamnatin Tarayya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Ministan Noma, Abubakar Kyari ya ce gwamnatin Bola Tinubu na tunanin rufe iyakar Najeriya ko kuma kara yawan samar da kayayyaki a kasar.

Ministan ya bayyana haka ne a yau Juma’a 9 ga watan Faburairu yayin ganawa da kwamitin Majalisar Dattawa a Abuja.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Sarkin Musulmi ya tura sako ga Hukumar ICPC kan boye abinci, ya dauki alkawari

Watakila Tinubu ya rufe iyakar Najeriya kan tsadar asbinci
Tinubu ya bayyana hanyoyin dakile tsadar abinci a Najeriya. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Mene ya ke cewa kan tsadar abinci?

Ya ce abin takaici ne yadda kasar ke fama da karancin abinci yayin da ake fita da abinci kullum zuwa kasashen ketare, cewar BusinessDay.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa kudin CFA ya fi karfin Naira a kasashe makusantar Najeriya wanda suke siyan kayan abinci da sauki.

A cewarsa:

“A yanzu CFA dubu daya ya kai naira 2,200 wanda a baya bai wuce naira 400 zuwa 500 ba shekarun baya.
“Saboda darajar naira ta zube, abincin kasarmu da araha ake siya a can kasashe makwabta wanda hakan yasa ake fita da abincin ba tsari.
“Muna kokarin samar da abincin a cikin gida da yawa saboda mu samar da shi ga mutane miliyan 230 da muke da su.”

Menene mafita kan tsadar abinci?

Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Najeriya vs Afrika ta Kudu: Jigon APC da wasu 'yan Najeriya 4 da suka kwanta dama yayin gasar AFCON

“Idan har hakan bai samu ba, dole mu rufe iyakar Najeriya gaba daya ko kuma mu samar da abincin ga sauran kasashen Afirka.”

Kyari ya ce fita da abincin ba bisa ka’ida ba shi ne babban matsalar da ya sa Najeriya ke fama da karancin abinci.

Ya ce sauran matsalolin sun hada da rashin tsari na gwamnatin Buhari kan noma da rashin tsaro da kuma matsalar tashin dala, cewar Politics Nigeria.

Legit Hausa ta ji ta bakin wani malami kuma masanin tattalin arziki.

Lamido Bello ya ce bai gamsu da wannan tsarin ba inda ya ba da hanyoyi uku da za a magance matsalar.

Ya ce:

"Hanya ta farko ita ce samar da tsaro ta yadda manoma za su iya yin noma wanda zai samar da abinci da kuma samar wa masana'antu kayan sarrafawa.
"Na biyu dole CBN ta sauya tsarin changing dala ta yi amfani da canji bai daya wato 'fixed exchange rate' madadin kasuwa ta yi halinta.

Kara karanta wannan

Kano: Yayin da ake cikin matsin tsadar rayuwa, gwamnati za ta dauki mataki kan masu boye abinci

"Na uku samar da wutar lantarki ingantacciya tare da bude iyakoki da gaggawa tare da janye haraji kan masu shigo da nau'in abinci."

Sultan ya bukaci daukar mataki kan abinci

Kun ji cewa Sarkin Musulmi, Sultan Sa’ad Abubakar ya bukaci hukumar ICPC da ta dauki mataki kan masu boye abinci.

Sultan ya ce boye abinci musamman wanda aka fi amfani da shi haramun ne kuma dai-dai ya ke da cin hanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel