AFCON: Ana Saura Kwana 4 Aurensa Ya Rasu, Cewar Iyalan Marigayi Ayuba a Kwara, Bayanai Sun Fito

AFCON: Ana Saura Kwana 4 Aurensa Ya Rasu, Cewar Iyalan Marigayi Ayuba a Kwara, Bayanai Sun Fito

  • A ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, ne Alhaji Ayuba Abdullahi, mataimakin Bursar na jami'ar jihar Kwara ya kwanta dama a yayin da yake kallon kwallon Najeriya da Afrika ta Kudu
  • 'Yan uwan marigayin sun bayyana cewa a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu ya kamata a daura masa aure kafin rai ya yi halinsa
  • Sai dai kuma, 'yan uwan nasa sun nuna dangana cewa koda babu wasan ba zai wuce wannan lokacin da Allah ya dibar masa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kwara - Rahotanni sun kawo cewa saura 'yan kwanaki a daura auren mataimakin Bursar na jami'ar jihar Kwara, Alhaji Ayuba Olaitan, wanda ya rasu yayin kallon wasan Najeriya da Afrika ta Kudu.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ta yiwu Tinubu ya rufe iyakar Najeriya kan karancin abinci, ya fadi sauran hanyoyi

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu, aka tsayar za a daura aurensa da sahibarsa kafin mutuwa ya riske shi.

Matakin da aka dauka na soke kwallo na biyu da Najeriya ta ci tare da buga fenariti ya jefa masoya da dama cikin zullumi da mamaki.

Ranar Lahadi ya kamata a daura auren marigayi Ayuba
AFCON: Ana saura kwana 3 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito Hoto: @DeeOneAyekooto/@NGSuperEagles
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A karshe dai, a kalla 'yan Najeriya biyar ne suka kwanta dama saboda wannan fargaba.

Tawagar Najeriya, wato 'yan wasan Super Eagles ne suka yi nasara a wasan da 4-2 kan fenariti.

Ranar Lahadi aurensa, 'yan uwan marigayin

Da yake magana da jaridar Daily Trust yayin addu'ar ukun mamacin a ranar Asabar, wani 'dan uwan marigayin, Mista Ayuba Akeem, wanda ya tabbatar da batun auren a ranar Lahadi, ya bayyana marigayin a matsayin "mai taimakon jama'a."

“Shi mutum ne mai kirki kuma ginshikin iyalin. Ya kasance mai alkhairi ga ’yan uwa, abokan siyasa da abokan aikinsa.

Kara karanta wannan

"Kada ka kalla idan kana da hawan jini": Matashi ya bada shawara gabannin wasan Najeriya na karshe

"Kuma a shirye yake kodayaushe don ya sanya murmushi a fuskar jama'a komai girman matsalar da mutane suka kawo masa.
"Kuma sabanin maganganun da ke yawo a waje, mun yarda cewa mutuwarsa nufi ne na Allah madaukakin sarki a wannan lokacin da kuma inda ya mutu amma ba don wasan ba.
"Ko da bai kalli wasan ba zai mutu a wannan lokacin," inji shi.

Shi ya tuka mu a wannan daren, abokiyar aikinsa

Haka kuma, wata 'yar uwarsa kuma abokiyar aikinsa, Aisha, wacce ya zanta da jaridar ta tuna cewa:

"Shine ya tuka mu zuwa gida a wannan rana daga Malete zuwa Ilorin.
"Ya kasance cikin koshin lafiya kuma tare muka ci abinci kafin muka baro ofis. Harma yana fada wa wasu abokan aikinsa cewa watakila ba zai kalli wasan ba saboda baya son abin da zai dame shi.
"Da muka isa wajen, an rigada an fara wasan sannan ya umurci dansa, Umar, da ya kunna janareto saboda babu wuta.

Kara karanta wannan

Najeriya vs Afrika ta Kudu: Jigon APC da wasu 'yan Najeriya 4 da suka kwanta dama yayin gasar AFCON

"Shine ya kunna talbijin, babu wata matsala ta jiri kuma a gida ya kalli wasan, ba gidan kallo ba.
"Ya kasance zaune kan kujera sannan ya jingina bayansa lokacin da dansa ya ce babana kana kallon abin da ke faruwa a wannan wasan?"
"Mun yarda cewa lokacin da Allah ya dibar masa zai mutu kenan wanda ya daidai da lokacin wasan."

Bukola Saraki ya dau nauyin karatun yaran mamacin

A yayin taron, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya ba biyu daga cikin yaran mamacin tallafin karatu kyauta.

Ya yi addu’ar Allah ya ji kan marigayin tare da yi masa addu'ar samun Aljannar Firdausi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel