Bidiyon Wata Amarya da Ta Yi Kwaliyyar Ban Mamaki Ya Girgiza Intanet, Angon Ya Firgita

Bidiyon Wata Amarya da Ta Yi Kwaliyyar Ban Mamaki Ya Girgiza Intanet, Angon Ya Firgita

  • Wata amarya ta girgiza jama'a bayan wani bidiyonta dauke da kwaliyya dambare a wajen bikinta ya bayyana a intanet
  • A cikin bidiyon, an gano ta tare da angonta, wanda ke kallonta cike da mamaki yayin da ake shagalin bikinsu
  • Yayin da ake cece-kuce a sashin sharhi, mutane da dama sun ce tsoro da firgici ya nuna karara a fuskar angon

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata amarya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya sakamakon irin kwaliyyar da ta yi a ranar bikinta.

Wani bidiyo da shafin tailorcataloguepage ya wallafa a Instagram ya nuno amaryar da angonta sanye da kaya iri guda kalar ruwan lemu.

Fuskar amaryar ta sha hoda
Bidiyon Wata Amarya da Ta Yi Kwaliyyar Ban Mamaki Ya Girgiza Intanet, Angon Ya Firgita Hoto: @tailorcataloguepage/Instagram
Asali: Instagram

Kwaliyyar amaryar ta yi hayaniya da yawa domin ko kusa bai dace da kalar fatarta ba. Ta yi amfani da kalar ruwan gwal da ruwan bula a idanunta sannan ta shafa kala daban a labban bakinta.

Kara karanta wannan

Hadadden saurayi 'dan shekaru 24 ya yi wuff da 'yar shekaru 80, tana matukar son shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hodar fuskarta ta yi yawa, lamarin da ya haddasa cece-kuce a tsakanin jama'a da suke ganin sam ba a kyauta mata ba.

Kalli bidiyon kwalliyar amaryar a kasa:

Jama'a sun yi martani kan kwalliyar amaryar

@nonnie_abraham:

"Ya zama dole a kama wasu masu kwalliyan gaskiya."

@miz_ivon:

"Yayin da tsohuwar budurwar mijinki ta yi maki kwalliya a ranar aurenki."

@tochukwujoyce:

"Wannan abin damuwa ne matuka."

@somasochi:

"Abokina lumshe ido idan kana bukatar taimako don tserewa."

@yaa_oba:

"Ina iya ganin tsoro karara a fuskar mijin...aah amma ta yaya aka yi ta bari aka yi amfani da fuskarta wajen gwaji a ranar aurenta?"

@sumadenikeclothings:

"Wannan ya yi yawa. Sai da na kalli hannaye da kafufuwan don tabbatar da fuskar."

@leemah_wine_and_liquor:

"Mijin cewa yake abin da na yi oda da wannan na samu."

Kara karanta wannan

Kogi: An tsinci gawar daliban kwaleji a dakin kwanansu, an gano abin da ya kashe su

Matashi ya yi wuff da 'yar shekaru 80

A wani labari na daban, wani matashi 'dan kasar Tanzaniya yana soyayya da tsohuwar da ta isa yin kaka da shi.

George 'dan shekaru 24 da Catherine Thomas, mai shekaru 80, sun kore dukkan shakku ta hanyar nuna cewa soyayya tana cin galaba akan komai, rahoton Afrimax English.

Asali: Legit.ng

Online view pixel