Hotunan amaryar da tayi biki ba tare da kwaliyya ba ya haddasa cece-kuce

Hotunan amaryar da tayi biki ba tare da kwaliyya ba ya haddasa cece-kuce

  • 'Yan Najeriya sun bayyana ra’ayinsu mabanbantan game da hotunan wata amarya da ta yi bikin aure ba tare da kwaliyya ba
  • Amaryar da angonta sun sanya kayan gargajiya mai launin kore a kyawawan hotuna
  • Wasu masu amfani da Twitter sun ce basu ga wani abun birgewa game da hakan ba yayinda abun ya birge wasu

Yayinda gaba daya aka yarda cewa aure shawara ne mai daɗi da masoya ke ɗauka don ƙarfafa dangantakar su, ma'auratan sune ke da zabi kan yadda suke so taron bikinsu ya kasance.

Hotunan bikin auren wasu ma'aurata 'yan Najeriya sun haifar da zazzafan muhawara a shafukan sada zumunta.

KU KARANTA KUMA: An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu

Hotunan amaryar da tayi biki ba tare da kwaliyya ba ya haddasa cece-kuce
Hotunan amaryar da tayi biki ba tare da kwaliyya ba ya haddasa cece-kuce Hoto: @SIR_YUYU
Asali: Twitter

A hotunan da @SIR_YUYU ya yada a shafin Twitter, yayin da ma'auratan da ba a san ko su wanene ba suka yi kyau a cikin kayan bikin aurensu masu launin kore, yanayin da amaryar ta bayyana ne ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu.

Kara karanta wannan

Abinda Yasa Nake Da Gwarin Guiwar Cewa Ni Zan Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023, Tinubu Ya Magantu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tayi ado tsaf cikin shiga ta alfarma ba tare da yin kwalliya a fuskarta ba.

Hotunan da shafin @SIR_YUYU ya wallafa na dauke da rubutu kamar haka: "wannan amaryar ta fita ba kwaliyya a ranar bikinta! "

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe akalla mutum 2600, sun karbi kudin fansan kimanin N1bn: Matawalle

Mawallafin ya kuma bi shi da sharhin cewa, 'ba ta mutu ba.'

@A_Abby_Abi ya yi martani da cewa:

''Ba ita bace ta farko ba kuma ba zata zama ta karshe ba.

"Hakanan, hakan bai sanya ta zama ta musamman ba. Ta dai yi abin da take so ne."

@Bholarjee ya mayarda martani:

"Idan ita da mijinta sunyi amanna da hakan, babu matsala.

"Dole ne matata ta yi kwaliyya ranar bikin mu. "Komai ra'ayi ne!"

Kara karanta wannan

ASUU Ta Dawo, Ma’aikatan Asibiti Sun Fara Barazanar Tafiya Yajin Aiki Nan da Kwana 7

A wani labarin, Biloniyan Nigeria kuma tsohon dan majalisar taraya, Cif Ned Nwoko, ya yi bayanin abin da yasa ya ke da matan aure fiye da daya kuma ya fi son auren 'yan mata.

A hirar da BBC Igbo ta yi da shi a ranar Laraba, jigon na PDP ya ce batun tattalin arziki ne yasa ya ke auren mata fiye da daya, Vanguard ta ruwaito.

Nwoko, mijin jaruman Nollywood Regina Daniels ya ce galibin dan arewa yana da mata a kalla guda biyu wanda ya ce hakan na hana mata yawon bin maza barkatai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel