Sabbin zafafan hotunan jikar Shugaban kasa Buhari sun bayyana

Sabbin zafafan hotunan jikar Shugaban kasa Buhari sun bayyana

  • Wasu kyawawan hotuna sun bayyana na jikar shugaban kasa Muhammadu Buhari wato Amal
  • Diyar shugaban kasar, Hadiza Bello Buhari ce ta haifi kyakkyawar budurwar
  • A hotunan wanda tuni ya karade shafukan soshiyal midiya, an gano matashiyar cikin shiga ta alfarma, yayin da ta yi kwalliya da ya bayyana sirrin kyawunta

Ko shakka babu cewa Allah ya azurta Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kyawawan yara mata na nunawa sa’a.

Kuma Hausawa sun ce barewa ba za ta yi gudu danta ya yi rarrafe ba, don haka suma yaran sun haifa masa kyawawan jikoki, kasancewar ahlin shugaban kasar sun gaji kyau ta wajen uwa da uba.

Sabbin zafafan hotunan jikar Shugaban kasa Buhari sun bayyana
Amal jika ce ga shugaban kasa Muhammadu Buhari Hoto: Linda Ikeji
Asali: UGC

Wasu zafafan hotuna sun bayyana na daya daga cikin kyakkyawan jikokin shugaban kasar mai suna Amal.

Kara karanta wannan

Sai irin su Buhari: Osinbajo ya bayyana wanda iya zai magance matsalar tsaro a Najeriya

Amal dai ta kasance daya daga cikin yara mata da Allah ya azurta diyar shugaban kasar, Hadiza Buhari Bello, da su.

A cikin hotunan, an gano kyakkyawar matashiyar sanye da doguwar riga fara da kuma kallabi daure a kanta, yayinda ta kawata fuskarta da kwaliyya wanda ya fito da sirrintaccen kyawun da take da shi.

Ga karin hotuna wanda shafin Linda Ikeji ya wallafa:

Sabbin zafafan hotunan jikar Shugaban kasa Buhari sun bayyana
Kyakkyawar jikar shugaban kasa, Amal Hoto: Linda Ikeji
Asali: UGC

Sabbin zafafan hotunan jikar Shugaban kasa Buhari sun bayyana
Sabbin zafafan hotunan jikar Shugaban kasa Buhari sun bayyana Hoto: Diya ce ga Hadiza Bello Buhari
Asali: UGC

Sabbin zafafan hotunan jikar Shugaban kasa Buhari sun bayyana
Sabbin zafafan hotunan jikar Shugaban kasa Buhari sun bayyana
Asali: UGC

Wannan fitsara ne: Malami ya yi tsokaci kan shigar da amaryar Yusuf Buhari tayi

A wani labari na daban, Babban Malamin addinin Islama, Dr Ibrahim Jalo Jalingo, ya yi tsokaci game da shigar da Zahra Bayero; amaryar Yusuf Buhari, yana mai nuna takaicin yadda 'ya'yan musulmai suka baci da shigar nuna tsiraici.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Magoya baya sun hada N10m don siyawa zabin Buhari fam

A lokacin bikin ne wasu hotuna suka watsu a kafafen sada zumunta, wadanda ke nuna Zahra Bayero, budurwar da dan shugaban kasa Buhari zai aura sanye da wasu kaya masu nuna wane bangare na jikinta.

Wannan shiga da tayi ya jawo cece-kuce, yayin da mutane da dama suka nuna damuwarsu da cewa, wannan shiga bata yi dace da addinin Islama ba, kamar yadda budurwar take musulma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel