Wata Matar Aure a Dubai Ta Ce Attajirin Mijinta Na Bata KSh Miliyan 37 Duk Wata Don Ta Wataya

Wata Matar Aure a Dubai Ta Ce Attajirin Mijinta Na Bata KSh Miliyan 37 Duk Wata Don Ta Wataya

  • Malaikah Raja daga kasar Birtaniya ta auri dan kasuwa Mohammed Fuaadh, kuma ma'auratan suna zaune ne a Dubai tare da dansu
  • Kyakkyawar matar bata aiki, kuma mijinta na bata KSh miliyan 37 duk wata a matsayin alawus domin kula da kanta
  • Tana kashe kudin wajen gyaran gashi, fatarta da gyaran jiki da kuma siyan kayan alatu da tsadaddun rigunan sawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matar aure da ke zaune a kasar Dubai ta girgiza intanet bayan ta bayyana cewa attajirin mijinta na bata KSh miliyan 37 duk wata a matsayin alawus.

Mata da mijinta
Wata Matar Aure Yar Dubai Ta Ce Attajirin Mijinta Na Bata KSh 37m Duk Wata Don Kula da Kanta Hoto: @malaikahraja.
Asali: Instagram

Yaya sunan mijin Malaika Raja?

A cikin wani bidiyo da ya dauka hankali a Instagram, Malaikah Raja ta bayyana yadda take kashe makudan kudade daga asusun mijinta, Mohammed Fuaadh.

Kara karanta wannan

Tsige yan majalisar PDP 23: Gwamnan Filato ya ziyarci Tinubu, ya yi karin bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Gaba daya alawus dina na siyayya shine KSh 800,000, siyan kayan kwalliya da alatu miliyan 2.4 sannan ina da wasu kadarori da ke kawo mun KSh miliyan 32, tausa duk sati KSh 162, 000, sannan ina gyaran farce da jiki kan KSh 80,000," inji Malaikah.

Ta kara da cewa:

"Alawus din gyaran gashina KSh miliyan 1.3, kan kwaliyya da mayukan gyaran jiki ina samun KSh 323, 000 sannan fitan yawon dare da cin abinci wannan babu iyaka. Idan ban kashe dukka kudaden ba, suna tafiya asusun ajiyata wanda yake zam."

Tana kammala bayar da labarinta, sai jama'a suka yi tururuwan zuwa sashinta na sharhi don bayyana ra'ayinsu game da tsarin rayuwarta.

Wasu na ganin sam yanayinta bai nuna tana kashe irin wannan kudin da ake bata ba, yayin da wasu suka nemi ma'auratan su karbi rikonsu.

Kara karanta wannan

Kano: Kwankwaso Ya faɗi makircin da aka Shirya ƙulla masa idan Gawuna ya yi nasara a Kotun Koli

Kalli bidiyonta a kasa:

Martanin masu amfani da soshiyal midiya

dianekrichie:

"Me yasa kike gyaran gashi idan har ba za ki iya nuna gashin naki ba?"

abrese16:

"Ni ba dan luwadi bani ko wani abu, amma shin mijinki na neman miji?"

famousmab_:

"Ta yaya zan nemi zama matar aure a Dubai?"

i_am_mora:

"Ta yaya bature ke zama matar Dubai?....ina taya wani abokina tambaya ne."

Matar aure ta shiga zullumin ranar haihuwa

A wani labari na daban, mun ji cewa wata mata mai juna biyu da ya tsufa sosai ta yi fice a dandalin TikTok bayan ta bai wa mata shawara mai ban dariya.

Matar mai juna biyu wacce aka kira da suna @omotarah5 a TikTok ta yada wani bidiyonta cikin tunani mai zurfi yayin da lokacin haihuwarta ke kara gabatowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel