Buhari Ya Tura Sako Mai Kama Hankali Bayan Rasuwar Tsohon Gwamna, Ya Fadi Dangantakarsu

Buhari Ya Tura Sako Mai Kama Hankali Bayan Rasuwar Tsohon Gwamna, Ya Fadi Dangantakarsu

  • Yayin da ake jimamin rasuwar tsohon gwamnan jihar Yobe, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi martani
  • Buhari ya bayyana cewa ya shiga rudani bayan samun labarin rasuwar marigayin wanda amininsa ne na gaskiya
  • Tsohon shugaban ya bayyana haka ne a shafinsa na X a yau Lahadi 4 ga watan Faburairu bayan rasuwar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammdu Buhari ya tura sakon jaje ga al'ummar jihar Yobe.

Buhari ya tura sakon ne bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Bukar Abba Ibrahim a yau Lahadi 4 ga watan Faburairu.

Buhari ya tura sakon jaje bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar Yobe
Buhari ya kadu bayan samun rasuwar Bukar Abba Ibrahim. Hoto: Muhammadu Buhari, Bukar Abba Ibrahim.
Asali: Facebook

Mene Buhari ke cewa kan rasuwar Abba?

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan rasuwar shahararren jarumin fina-finai a Najeriya da shekaru 81

Tsohon shugaban ya bayyana haka ne a shafinsa na X a yau Lahadi 4 ga watan Faburairu bayan rasuwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya kadu da samun rasuwar jigon jam'iyyar APC kuma gwamnan farar hula na farko a jihar Yobe.

Ya ce:

"Na kadu sosai da samun rasuwar Sanata Bukar Abba Ibrahim, ina mika sakon ta'aziyya ga iyalansa da ya bari.
"Ina kuma tura sakon jaje ga gwamnatin jihar da kuma jama'ar jihar Yobe gaba daya.
"Dalilin mutuwarsa, na rasa babban amini wanda na sani fiye da shekaru da muke yawan tattauna matsaloli."

Buhari ya ce kwarewar marigayin a sanin mutane da ya mulka ba zai misaltuba, inda ya yi addu'ar Allah ya masa rahama.

Marigayin ya rasu ne a yau Lahadi 4 ga watan Faburairu a kasar Saudiyya ya na da shekaru 73 a duniya, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda aka binne marigayi tsohon gwamnan Arewa bayan jana'izarsa a masallacin Harami

Sanatan ya kasance tsohon gwamnan jihar daga shekarar 1999 zuwa 2007 bayan ya mulki jihar a shekarar 1992 zuwa 1993.

Bukar Abba ya riga mu gidan gaskiya

Kun ji cewa Tsohon gwamnan jihar Yobe, Bukar Abba Ibrahim ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne a Saudiyya bayan ya sha fama da jinya kamar yadda wata majiya ta tabbatar a yau ranar Lahadi, 4 ga watan Fabrairu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ya na da shekaru 73 a duniya bayan shan fama da jinya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel