An Yi Rashi a Arewa: Tsohon Gwamnan Jihar Yobe Ya Rasu Yana da Shekara 73 a Duniya

An Yi Rashi a Arewa: Tsohon Gwamnan Jihar Yobe Ya Rasu Yana da Shekara 73 a Duniya

  • Tsohon gwamnan jihar Yobe, Bukar Abba Ibrahim ya rasu a wani asibiti da ke birnin Makkah na ƙasar Saudiyya sakamakon rashin lafiya da ya yi fama da shi
  • Bukar Abba ya yi gwamnan jihar Yobe har sau uku, inda aka fara rantsar da shi a jamhuriya ta uku, sannan sai shekarar 1999 da 2003
  • Tsohon gwamnan ya kuma taɓa zama sanata, ya bar mata biyu da ƴaƴa 17, ɗaya daga cikin matansa ƴar majalisa ce a yanzu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Saudiyya - Tsohon gwamnan jihar Yobe, Bukar Abba Ibrahim ya rasu.

Marigayin ya rasu ne a ƙasar Saudiyya bayan ya sha fama da jinya kamar yadda wata majiya ta shaida wa Daily Trust a ranar Lahadi, 4 ga watan Fabrairun 2024.

Kara karanta wannan

Sanata ya fallasa yadda wasu 'Hadimai' suka talauta dukiyar Najeriya a mulkin Buhari kafin 2023

Bukar Abba Ibrahim ya rasu
Tsohon gwamnan ya rasu ne a Saudiyya Hoto: Concerned Nigeria
Asali: Twitter

Jaridar Sahara Reporters ta kawo rahoton rasuwar marigayin wanda ya rasu yana da shekara 73 a duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani majiya na kusa da iyalan tsohon gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Sen. Bukar Abba Ibrahim ya rasu a yanzu haka a Makkah, Allah ya yi masa rahama ya kuma sa Jannatul Firdaus ta zama masaukinsa na ƙarshe Amin Thumma Amin."

Tarihin marigayi Bukar Abba Ibrahim

Ibrahim yayi gwamnan jihar Yobe daga watan Janairu 1992 zuwa Nuwamba 1993 a jamhuriya ta uku.

A farkon jamhuriya ta huɗu, an sake zaɓe shi a ƙarƙashin inuwar rusasshiyar jam’iyyar ANPP a 1999 kuma ya yi wa’adi biyu.

A shekarar 2007 ne aka zaɓe shi a matsayin Sanatan Yobe ta gabas sannan a shekarar 2019 ya haƙura da yin takara ya bar ministan ƴan sanda na yanzu Ibrahim Geidam ya nemi kujerar sanatan.

Kara karanta wannan

Duk da suka daga 'yan Arewa ministan Tinubu ya dage kan mayar da FAAN zuwa Legas, ya fadi dalili

Mata da ƴaƴa nawa Marigayi Bukar Abba Ibrahim ya bari?

Tsohon gwamnan ya rasu yana da shekaru 73 bayan doguwar jinya. Ya rasu ya bar mata biyu da ƴaƴa 17.

Ɗaya daga cikin matansa ita ce mamba mai wakiltar Tarmuwa/Gulani/Damaturu/Gujba kuma tsohuwar ƙaramar ministar harkokin waje, Khadija Bukar Abba Ibrahim.

Shugaban Ƙasan Namibia Ya Rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasan Namibia, Hage Geingob, ya yi bankwana da duniya.

Marigayin wanda ya rasu a ƙasar Amurka, ya rasu ne yana da shekara 82 a duniya bayan ya yi fama da jinya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel