Bidiyon Yadda Aka Binne Marigayi Tsohon Gwamnan Arewa Bayan Jana'izarsa a Masallacin Harami

Bidiyon Yadda Aka Binne Marigayi Tsohon Gwamnan Arewa Bayan Jana'izarsa a Masallacin Harami

  • Yayin da ake ci gaba da jimamin rasuwar tsohon gwamnan Yobe, Bukar Abba, an binne marigayin a kasar Saudiyya
  • An gabatar da sallar jana'izar marigayin a masallacin Harami jim kadan bayan idar da sallar asuba a cikin masallacin
  • Wannan na zuwa ne bayan rasuwar tsohon gwamnan a jiya Lahadi 4 ga watan Faburairu a kasar Saudiyya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Makka, Saudiyya - An binne marigayi tsohon gwamnan Yobe, Bukar Abba Ibrahim a kasar Saudiyya.

Tsohon gwamnan ya rasu ne a jiya Lahadi 4 ga watan Fabrairu a Saudiyya bayan ya sha fama da jinya na tsawon lokaci.

An binne marigayi tsohon gwamnan Yobe a kasar Saudiyya
A jiya ne aka sanar da rasuwar Bukar Abba Ibrahim. Hoto: Bukar Abba Ibrahim.
Asali: Twitter

Yaushe aka binne tsohon gwamna, Bukar?

Kara karanta wannan

An shiga rububi, Gwamnatin Tinubu ta magantu kan yadda za ta daga darajar Naira a kan dala

Zagazola Makama ya tabbatar da cewa an gudanar da sallar jana'izarsa a masallacin Harami bayan gabatar sallar asuba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bukar Abba ya mulki jihar a shekarar 1999 zuwa 2007 bayan dawowa mulkin dimukradiyya a Najeriya.

Bayan kammala mulkin jihar, Bukar ya yi nasarar zama sanata Majalisar Dattawa na tsawon shekaru.

Bukar shi ne gwamnan farar hula na farko a Yobe

A jiya Lahadi ce 4 ga watan Faburairu aka sanar da rasuwar marigayin a Saudiyya ya na da shekaru 73 a duniya.

Marigayin shi ne gwamnan farar hula na farko inda ya mulki jihar a shekarar 1992 zuwa 1993 a jihar.

Daga bisani ya zama gwamnan jihar bayan dawowar dimukradiyya a Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2007, cewar Premium Times.

Har ila yau, Sanatocin daga Arewacin Najeriya sun mika sakon jaje ga iyalan marigayin a jiya Lahadi 4 ga watan Faburairu.

Kara karanta wannan

Buhari ya tura sako mai kama hankali bayan rasuwar tsohon gwamna, ya fadi dangantakarsu

Sanata sun nuna alhini tare da addu'ar ubangiji ya yi masa rahama da tabbatar da shi a gidan ajanna firdausi.

Buhari ya mika jaje kan rasuwar Bukar Abba

Kun ji cewa, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tura sakon jaje ga iyalan marigayi Bukar Abba Ibrahim.

Buhari ya bayyana rasuwar a matsayin babbar rashi a gare shi musamman kasancewar marigayin babban amininsa ne.

Tsohon shugaban ya nuna alhini tare da mika sakon jaje ga gwamnatin jihar da kuma al’ummar jihar Yobe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel