An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina

An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina

  • Jami'an 'yan sanda a jihar Katsina sun yi ram da wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne su biyu
  • Dubun masu laifin ya cika ne a yayin da suke kokarin karbar kudin fansa bayan sun yi barazanar sace wasu mutane
  • Kakakin 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah ne ya bayyana a wani taron manema labarai

Katsina - Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta kama wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne su biyu, Channels TV ta rahoto.

An kama daya daga cikin masu laifin mai suna Saifullahi Usman dan shekara 32 na Unguwar Amare da ke karamar hukumar Malumfashi, a ranar 24 ga watan Disamba.

An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina
An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ta kwabewa wanda ake zargin ne lokacin da ya boye lambar wayarsa sannan ya kira wani Shafi’u Mohammed na unguwar Kililin, inda ya yi barazanar kashe shi ko garkuwa da shi ko kuma danginsa idan bai biya kudin fansa N50,000 ba.

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

Kakakin 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya bayyana a taron manema labarai cewa jami'an rundunar sun kama wanda ake zargin ne a inda ya je daukar kudin fansar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi bayanin cewa a yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya kara da cewa har yanzu bincike na gudana.

A rahoton Daily Post, rundunar ta kuma ce ta yi nasarar kama wani mai garkuwa da mutane, Muhammed Ibrahim, mai shekaru 30 daga kauyen Kagara a karamar hukumar Kafur na jihar.

Wanda Ibrahim yayi wa barazana, Bello Umar na kauyen Mahuta a karamar hukumar ya kai kara ofishin yan sandan Kafur cewa ya samu wani rubutaccen sako, inda aka yi masa barazana da ya biya N100,000 ko kuma a sace shi ko kashe shi.

A yayin bincike ne aka gano wanda ake zargin sannan aka kama shi inda ya amsa laifinsa.

Kara karanta wannan

An damke wani matashin dan bindiga yana kokarin tare hanya, an ceto mutum 10 daga hannunsa

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

A wani labarin kuma, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.

An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Mai magana da yawun yan sanda, SP Gambo Isah, wanda ya yi holen Tijanni a gaban manema labarai ya ce an dauki mataki a kansu ne bayan yan matan Katsina da dama sun shigar da korafi a kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel