Yan kungiyar Boko Haram sun sace dabbobi da abinci

Yan kungiyar Boko Haram sun sace dabbobi da abinci

- Boko haram sun kai wani sabon hari a kauyen Dile dake karamar hukumar Askira-uba a jahar Borno.                                                                                                                                                                              -Shaidun da abun ya faru a gaban su, sun ce yan ta'addan sun kone wurare da dama inda suka kwashe dabbobi da kuma kayan abinci.

Abun mamakin shine yawancin yan kauyen sun boye a tsaunika da dajin dake kusa da kauyen. Harin da aka baiyana cewar ya tada hankali kwarai kuma sun lalata abubuwa da dama daya shafi gidaje da kuma sace masu kayan abinci da dabbobin su.

KU KARANTA : Manyan laifuka 6 da ake aikatawa a Najeriya

A lokacin harin yawancin yan kauyen sun buya a tsaunika da dajin dake kusa da kauyen, inda suka gode sakamakon rashin samun su da yan ta'addan basuyi. A lokacin da wakilan mu suka zatta da wani mazauna kauyen Clement Saturami, wanda yayi musu karin haske dangane da kai harin.

Yan kungiyar Boko Haram sun sace dabbobi da abinci
Boko Haram

 

Acewar Satumari, yan ta'addan sun shigo kauyen ne sunata harbe harbe, alokacin kowa ya gudu daman daga kauyen kafin suzo, sai dai sun kashe mutum daya, wani yaron marigayi mai unguwan gari daya dade da rasuwa. Yayon da ake kira da suna (Lawal) wanda suka sameshi yana bacci sakamakon tatil da yayi da giya, inda suka kashe shi har lahira.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel