'Yan Bindiga Sun Tafka Mummunar Ɓarna, Sun Sace Mata Sama da 35 Tare da Kashe Wasu a Arewa

'Yan Bindiga Sun Tafka Mummunar Ɓarna, Sun Sace Mata Sama da 35 Tare da Kashe Wasu a Arewa

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai mummunan hari kauyen Magizawa da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Zamfara
  • Mazauna yankin sun tabbatar da cewa maharan sun sace mutane 50 ciki harda mata 36 kana sun kashe rayuka 3
  • Rahoto ya nuna ƴan banga sun yi kokarin daƙile harin amma maharan sun ci karfinsu da makamai manya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane kimanin 50 daga cikinsu harda mata 36 a kauyen Magizawa da ke karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara.

‘Yan bindigan, waɗanda suka kai hari kauyen ranar Lahadi sun kuma kashe mutane uku ciki har da dan kungiyar ‘yan banga tare da jikkata wasu biyar.

Kara karanta wannan

Tsageru sun farmaki motar kamfen mataimakin gwamnan PDP, sun tafka mummunar ɓarna

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.
Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka, Sun Sace Mata Akalla 36 a Jihar Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Yadda ƴan banga suka yi ƙoƙarin dakile harin

Wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ‘yan bindigar sun shiga kauyen ne da daddare lokacin da mafi akasarin mutane sun kwanta barci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rahoton Daily Trust, mutumin ya yi bayanin cewa, suna shiga kauyen, suka fara harbe-harbe a iska, wanda hakan ya sa mazauna garin suka tsorata.

A cewarsa, bayan tsorata jama'a da harbe-harbe ne sai ƴan bindigan suka fara shiga gida-gida suna binciken mutanen da suka je ɗauka.

A kalamansa ya ce:

"Ko da yake muna da ’yan banga da ke sintiri a kauyen da daddare, amma ‘yan bindigan sun fi ‘yan banga yawa. Maharan sun zo da adadi mai yawa kuma ɗauke da makamai.
"Yan banga na yankin sun yi iya kokarinsu, amma a karshe ‘yan bindigar sun kashe daya daga cikinsu da wasu mutum biyu a harin.”

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka bankawa fadar fitaccen basarake wuta a Najeriya

A ruwayar Vanguard, wani mazaunin garin na daban wanda shi ma baya son a buga sunansa ya ce:

"Muna zargin imfoma ne suka haddasa wannan harin saboda yan bangan mu suna kokari koda yaushe a ankare suke amma wannan karon ƴan bindigan sun shammace su.
"Muna tunanin imfomomin ne suka bai wa yan bindigan labarin yanayin aikin ƴan bangar a ranar da suka kawo harin shiyasa suka yi nasara."

Ko ƴan bindigan sun nemi kuɗin fansa?

Da aka tambaye shi ko maharan sun tuntubi dangin da abin ya shafa, ya tabbatar da cewa kawo yanzu babu daya daga cikin iyalan da ‘yan fashin suka kira domin neman kudin fansa.

Yayin da aka nemi jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan Zamfara, SP Yazid Abubakar, ya buƙaci a tuntuɓi mai magana da yawun rundunar Operation Hadarin Daji.

Ƴan Bindiga Suka Bankawa Fadar Fitaccen Basarake Wuta

A wani rahoton kuma wasu tsagerun ƴan bindiga sun ƙona fadar basaraken garin Isseke da ke ƙaramar hukumar Ihiala a jihar Anambra.

Basaraken mai suna, Igwe Emmanuel Nnabuife, ya ce maharan sun lalata komai na gidan wanda ya shafe shekaru yana ginawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel