Pantami Ya Samo Wanda Zai Biya Kudin Fansa a Sako ’Yan Uwan Nabeeha da Aka Sace a Abuja

Pantami Ya Samo Wanda Zai Biya Kudin Fansa a Sako ’Yan Uwan Nabeeha da Aka Sace a Abuja

  • Rahoton da muke samu ya bayyana matakind a Farfesa Pantami ya dauka wajen ganin an kubutar da ‘yan uwan marigayiya Nabeeha
  • Pantami ya ce ya samar da kudaden da za a ba ‘yan ta’adda domin tabbatar da an sako wadannan ahali da aka sace a makon jiya
  • Ana yawan sace mutane a Najeriya, musamman yadda ‘yan ta’addan ke amfani da zamani wajen tabbatar da karbar kudin fansa

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

FCT, Abuja - Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana yadda ya kawo hanyar sharewa ahalin Nabeeha hawaye bayan samo wanda zai biya kudin fansan da ‘yan bindiga suka nema bayan sace su.

Idan baku manta ba, an ruwaito yadda wasu ‘yan ta’adda suka yi awon gaba da wasu ‘yan gida daya ‘yan mata shida, inda suka nemi kudin fansan miliyoyin kudade.

Kara karanta wannan

Tsohon sanata ya shiga tashin hankali bayan 'yan damfara sun kwace WhatsApp dinsa

Wannan lamari ya dauki hankalin ‘yan Najeriya da dama, musamman ganin ya faru ne a babban birnin tarayya Abuja, inda ya fi ko ina tsaro a kasar.

Pantami ya samar da mafita ga wadanda aka sace
An samu mai biyan kudin fansan su Nabeeha | Hoto: @affantech1
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Pantami ya bayyana abin da ke ransa kan ba da fansa

Da yake bayyana yunkurin taimakawa ahalin da suka shiga jimami, babban malamin addinin Islama, tsohon minista kuma mai fada a ji a Najeriya, Farfesa Pantami ya samar da mafita.

Ya bayyana cewa, ya magantu da abokinsa da ya amince da biyan akalla Naira miliyan 50 don tabbatar da an sako wadannan ahali da ke hannun ‘yan ta’adda.

A bayaninsa, ya ce sam ba ya goyon bayan a ba ‘yan ta’adda kudaden fansa, amma yanayi ya nuna an cutar da ahalin kuma ya kamata a yi hubbasa don taimaka musu.

Dan uwa, abokin Pantami ya share hawayen Musulmai

Kara karanta wannan

Bayan shiga har wata kasa da kashe mataimakin shugaban Hamas, Isra'ila ta yi awon gaba da danginsa

A jawabinsa da ya yada a kafar Twitter, Pantami ya ce:

“Ni kaina ba na goyon bayan biyan kudin fansa ga ‘yan ta’adda. Sai dai kuma tunda ta tabbata jiya mun rasa ‘yarmu Nabeeha, kuma an yiwa sauran yaran 5 barazana kamar yadda na yi magana da mahaifinsu jiya da yau.
“Don haka, na yi magana da wani abokina kuma ɗan’uwa wanda ya amince zai biya sauran Naira miliyan 50 na miliyan 60 din nan take.
“Na ba da lambar asusun mahaifin ƴan matan mai suna, Mansoor Al-Kadriyar, ga abokina kuma dan uwa don aikawa da kudin kai tsaye. “

Ya za a yi da sauran kudaden da suka hau kai?

Pantami ya ba da shawari da ishara ga mahaifin ‘yan matan da cewa:

“Duk wani karin kudin da aka samu ya zuwa jiya, sai uban ya yi amfani da shi wajen yiwa yaran da sauran 'yan uwa a ahalin jinya da yardar Allah.

Kara karanta wannan

"Kada ku tsinewa shugabanninmu": Sarkin Musulmi ya aika muhimmin sako ga yan Najeriya

“Allah Ta'ala Ya sakawa wannan aboki kuma dan uwa da Jannatul Firdaus bisa wannan gudummawar. Ya kuma sakawa duk wadanda suka bada gudumawa ta kowace hanya da Jannatul Firdaus.
“Ya kuma gafartawa Nabeeha, ya kubutar da ‘yan uwanta. Allah kuma ya taimaki jami'an tsaronmu wajen kawo karshen wannan kalubale. Allah ya sa Najeriya ta zama wuri mafi alheri garemu baki daya.”

An kashe daya daga cikin ‘yan matan da aka sace

A bangare guda, Sherifdeen Al-Kadriyar, kawun yarinyar da yan bindiga suka kashe bayan sun yi garkuwa da ita da yan uwanta biyar a makon jiya a Abuja, ya bayyana yadda aka samu labarin rasuwar Nabeeha.

Jaridar Daily Trust ta rahoto yadda yan bindiga suka yi garkuwa da Nabeeha, mahaifinta da yan uwanta a yankin Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja, a daren ranar Talata.

Yan bindigar sun bindige wani kawun marigayiyar, Alhaji Abdulfatai, wanda ya jagoranci yan sanda wajen ceto su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.