Yan Bindiga Sun Kashe Daya Daga Cikin Mata 6 ’Yan Gida Daya da Suka Sace a Abuja

Yan Bindiga Sun Kashe Daya Daga Cikin Mata 6 ’Yan Gida Daya da Suka Sace a Abuja

  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kashe wata Nabeeha Al-Kadriyar da suka yi garkuwa da ita a birnin tarayya Abuja
  • Yan bindigar sun kashe Nabeeha ne a ranar Juma'a bayan da mahaifinta Alhaji Mansoor Al-Kadriyar ya gaza kai kudin fansarsu
  • Tun da fari dai an ruwaito yadda 'yan bindigar suka sace Alhaji Mansoor da 'ya'yansa shida a Abuja kuma suka nemi naira miliyan 60 kudin fansa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Yan bindiga da suka sace Alhaji Mansoor Al-Kadriyar tare da 'ya'yansa shida a Abuja, sun kashe daya daga cikin yaran.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun kashe yarinyar mai suna Nabeeha Al-Kadriyar a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Jam’iyyun adawa sun cigaba da shirin hada kai domin yakar Tinubu da APC a 2027

Yan bindiga sun kashe Nabeeha Al-Kadriyar
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun kashe Nabeeha Al-Kadriyar a ranar Juma'a. Hoto: @AmnestyNigeria
Asali: Twitter

The Nation ta ruwaito cewa tuni aka yi wa Nabeeha sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nabeeha da 'yan uwanta 5 ne 'yan bindiga suka sace

Nabeeha dai ta kasance dalibar aji hudu ce a bangaren nazarin kimiyyar kwayoyin halitta a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Tun da fari dai, 'yan bindigar sun saki maahaifin yaran, inda suka nemi ya kai masu naira miliyan 60 don sakin 'ya'yan nashi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai ba a kai ga hada kudin ba ne 'yan bindigar suka kashe Nabeeha, lamarin da ya hankalin 'yan Najeriya tare da samun tofin 'Allah ya tsine'.

An yi garkuwa da Alhaji Mansoor da 'ya'yansa a daren ranar Talata a karamar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja, inda suka nemi karin naira miliyan 40.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace malamin jami’ar tarayya a Zamfara

Ana neman taimako don kubutar da sauran matan

Kanin Alhaji Mansoor mai suna Abdulfatai wanda ya jagoranci 'yan sanda wajen dakile sace dan uwan nasa, ya gamu da ajalinsa bayan da 'yan bindigar suka harbe shi har lahira.

The Punch ta ruwaito cewa biyo bayan kashe Nabeeha, iyalan Alhaji Mansoor sun nemi taimakon 'yan Najeriya wajen ganin an hada wadannan makudan kudade da 'yan bindigar ke nema.

Rundunar. 'yan sanda ta bakin kakakinta Muyiwa Adejobi ya ce rundunar da sauran jami'an tsaro na aiki tukuru don ganin an kubutar da sauran yaran biyar.

Yan bindiga sun sace malamin jami'a a Zamfara

A wani labarin kuma, 'yan bindiga sun kutsa har cikin gidan Bello Janbako, wani malamin jami'ar tarayya Gusau, jihar Zamfara inda suka yi awon gaba da shi.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun sace malamin ne a ranar Larabar da ta gabata, bayan yin artabu da 'yan sandan da suka yi kokarin dakatar da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.