Atiku Ya Yi Martani Yayin Da Ƴan Bindiga Suka Halaka Nabeeha a Abuja

Atiku Ya Yi Martani Yayin Da Ƴan Bindiga Suka Halaka Nabeeha a Abuja

  • A yayin da a ke juyayin kisan gillar da aka yi wa Nabeeha Al-Kadriyar, Atiku Abubakar ya yi martani kan kisan da aka yi mata
  • Martanin na Atiku Abubakar ya jaddada bukatar sake duba tsarin tsaron ƙasar nan cikin gaggawa domin daƙile ayyukan ta'addanci
  • Nabeeha, ɗaliba ƴar 400L, ta gamu da ajalinta a hannun masu garkuwa da mutane, bayan sun sace ta tare da ƴan uwanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya mayar da martani kan rasuwar Nabeeha Al-Kadriyar.

Atiku Abubakar ya bayyana alhininsa kan rasuwar Nabeeha.

Atiku ya yi martani kan kisan Nabeeha
Atiku ya nuna alhininsa kan kisan Nabeeha Hoto: @atiku, @TheNationNews
Asali: Twitter

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, ƴan bindigar da suka yi garkuwa da Alhaji Mansoor Al-Kadriyar da ƴaƴansa shida, sun kashe ɗaya daga cikinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindigan sun halaka Nabeeha ne a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu.

Atiku ya yi martani kan rasuwar Nabeeha

Rasuwar Nabeeha ta haifar da ɓacin rai a shafukan sada zumunta musamman “X” (wanda aka fi sani Twitter a baya).

Da yake mayar da martani, Atiku ya bayyana matukar baƙin cikinsa kan rasuwar Nabeeha.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar a wani gajeren rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, @atiku a ranar Lahadi, 14 ga watan Janairu, 2024, ya buƙaci jami’an tsaro ciki har da ƴan sanda da su ƙara ƙaimi domin kuɓutar da ƴan uwan ​​Nabeeha daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Atiku ya rubuta a a shafinsa na Twitter cewa:

"Na ji baƙin ciki kan rahotannin kisan gillar da aka yi wa Nabeeha Al-Kadriyar, wacce aka yi garkuwa da ita tare da ƴan uwanta, kuma ta shafe kusan makonni biyu a hannun waɗanda suka sace su."

"Wannan kuma wani abin tunatarwa ne cewa masu garkuwa da mutane da ƴan bindiga suna gudanar da ayyukansu ba tare da wata tangarda ba a ƙasarmu, akwai bukatar a sake fasalin tsaro domin daƙile su ta yadda za a samu tsaron rayuka da dukiyoyi.
"Ya kamata jami'an tsaro su ƙara zage damtse domin ceto ragowar sauran waɗanda suke a hannun masu garkuwa da mutanen.
"Ina rokon Allah ya jikan marigayiyar da rahama ya kuma iyalanta haƙuri. - AA"

Atiku Ya Yi Jimamin Rasuwar Sheikh Giro

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi jimamin rasuwar Shiekh Giro Argungun.

Atiku ya ce Sheikh Giro na daga cikin manyan-manyan malaman addinin Musulunci da ake girmamawa a Najeriya da Yammacin Afrika baki daya, saboda irin gudummawar da ya ba da.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng