“Kada Ku Tsinewa Shugabanninmu”: Sarkin Musulmi Ya Aika Muhimmin Sako Ga Yan Najeriya

“Kada Ku Tsinewa Shugabanninmu”: Sarkin Musulmi Ya Aika Muhimmin Sako Ga Yan Najeriya

  • Mai martaba sarkin Musulmi ya ja hankalin yan Najeriya kan muhimmancin hadin kai don ci gaban kasa
  • Sultan na Sakkwato ya bukaci yan Najeriya da su daina la'antar shugabanni don kada abun ya shafi kasar
  • Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ce wajibi ne a matsayinsu na yan kasa masu kishin kasa su mutunta shugabanni da doka da oda don a zauna lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Mai girma sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya yi jan hankali ga yan Najeriya kan hadin kai da zaman lafiya a tsakani domin bunkasa da ci gaban Najeriya, rahoton Vanguard.

Sultan na Sakkwato ya yi wannan kiran ne a ranar Asabar, 13 ga watan Janairu, yayin da yake bude masallacin da aka sanyawa sunan Alhaji Abdullahi Habib a jami'ar tarayya ta Lokoja.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Gida-Gida ya aika muhimmin sako ga Gawuna bayan hukuncin Kotun Koli

Sarkin Musulmi ya ja hankalin yan Najeriya kan shugabanni
“Kada Ku Tsinewa Shugabanninmu”: Sarkin Musulmi Ya Aika Muhimmin Sako Ga Yan Najeriya Hoyo: @daily_trust
Asali: Twitter

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya rahoto cewa wata mata da mijinta ya rasu, Dr Maimuna Abdullahi, ce ta gina tare da bayar da gudunmawar masallacin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sultan wanda ya samu wakilcin Sarkin Keffi, Shehu Chindo-Yamusa III, ya ce wannan abun a yaba ne.

A cewarsa, a matsayin yan kasa masu kishin kasa, ya kamata yan Najeriya su koyi mutunta shugabanni da bin doka da oda, domin al’ummar kasar su samu alkiblar rayuwa.

Plantinum Post ta nakalto Sultan yana cewa:

“Ya kamata mu yi wa shuwagabannin mu addu’a sannan kada mu la’ance su, don kada su lalace, ta yadda za mu cutu a matsayinmu na kasa.
“Shi ya sa wasu iyali da ke kaunar Allah suka gina tare da bayar da gudunmawar wannan wurin ibadar don wasu su san Shi da kuma bauta Masa don jin dadinsu.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi shagube ga Betta kan alkawarinta na fitar da yan Najeriya miliyan 50 daga talauci

"Addu'ata ita ce Allah ya sakawa iyalan Habib da alkhairi ya kuma bai wa wasu sha'awa da himma don yin hakan don amfanin al'umma."

Sarkin Musulmi ya magantu kan hare-hare

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa mai martaba sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya diga ayar tambaya kan fikirar jami'an tsaron Najeriya biyo bayan hare-haren da ake kaiwa jihohin kasar.

Ya ce 'yan bindiga da masu aikata laifi kullum na shammatar jami'an tsaro yayin kai farmaki, wanda nakasu ne ga fikirar tattara bayanan jami'an.

Mai girma sarkin Musulman ya yi wannan maganar ne ranar Laraba a Bauchi, yayin gudanar da taron bitar da'awar Islama na kasa karo na 80, inda ya yi Allah wadai da harin Filato.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng