Bayan Hukuncin Kano da Plateau Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci Kan Karar Neman Tsige Gwamnan PDP

Bayan Hukuncin Kano da Plateau Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci Kan Karar Neman Tsige Gwamnan PDP

  • Kotun Ƙoli ta tanadi hukunci kan ɗaukaka ƙarar da ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Rivers ya yi kan nasarar Gwamna Fubara na PDP
  • Tonye Cole ya shigar da ƙarar ne a gaban kotun domin ƙalubalantar ayyana Gwamna Fubara a matsayin wanda ya lashe zaɓen da INEC ta yi
  • Kotun mai alƙalai biyar ta tanadi hukuncinta ne a yau Litinin, 15 ga watan Janaitu bayan kammala sauraron bayanan dukkanin ɓangarorin da shari'ar ta shafa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kotun Ƙoli ta tanadi hukunci kan ƙarar da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Rivers, Patrick Tonye-Cole ya shigar a kan hukumar INEC, jam'iyyar PDP da Gwamna Siminalayi Fubara.

Kara karanta wannan

Kotun koli ta yanke hukuncin ƙarshe kan ƙarar da aka nemi tsige gwamnan PDP daga mulki

Ƙarar ta Tonye Cole dai na zuwa ne bayan kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar da ya shigar kan cewa ba ta cancanta ba, da rashin gamsassun hujjoji, cewar rahoton Channels tv.

Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan Rivers
Gwamna Fubara ya kusa sanin matsayarsa a shari'ar zaben gwamnan Rivers Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Tonye Cole
Asali: Facebook

Tonye-Cole dai ya shigar da ƙara ne a kan Gwamna Fubara cewa bai yi murabus a matsayin Akanta Janar na jihar ba a cikin wa'adin da kundin tsarin mulki da dokar zaɓe ta ƙayyade.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Don haka, Tonye-Cole ya nanata cewa Fubara bai cancanci tsayawa takara ba, balle INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

Kotun Ƙoli ta tanadi hukunci

Kotun mai alƙalai mutum biyar ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun ta tanadi kan hukunci kan ɗaukaka ƙarar bayan dukkan bangarorin da ke cikin ƙarar sun kammala bayanansu, rahoton The Nation ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Yadda shugaban kasa Tinubu ya taka rawa a hukuncin Kotun Koli na zaben gwamnonin Kano da Plateau

Kotun kolin ta kuma yi watsi da ƙarar da Innocent Kere na jam’iyyar Allied People’s Movement (APM) ya shigar bayan lauyansa ya janye ƙarar.

Kotu Ta Yi Watsi da Ƙarar Tonye Cole

A baya rahoto ya zo cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Rivers, ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Tonye Cole ya shigar kan zaɓen gwamnan jihar.

Cole ya garzaya gaban kotun ne yana ƙalubalantar matakin INEC na ayyana ɗan taƙarar PDP, Mista Fubara, a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Ribas bayan kammala zaɓe

Asali: Legit.ng

Online view pixel