Yanzu-yanzu: Hadimin Atiku na kut-da-kut ya rasu

Yanzu-yanzu: Hadimin Atiku na kut-da-kut ya rasu

Umar Pariya, daya daga cikin shakikan hadiman tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya rasu.

Mista Pariya ya rasu ne da safiyar Talata a kasar Dubai bayan gajeriyar rashin lafiya.

Wata majiya daga iyalan mamacin ta sanar da jaridar Daily Nigerian cewa, mamacin ya kasance rai a hannun Allah tun makonni biyu da suka shude.

Umar Pariya yana daya daga cikin na kusa da Atiku da suka masa rakiya zuwa kasar Amurka a watan Janairun 2019 gabanin babban zaben kasa na shekarar tare da shugaban majalisar dattawa na wancan lokacin, Dakta Bukola Saraki da wasu na kusa da shi.

Ku saurari karin bayani ...

DUBA WANNAN: Daga karshe: Buhari ya warware sarkakiyar sallamar hadiman Osinbajo 35

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel