Jigon NNPP Ya Fadi Abu 1 da Zai Faru da Alkalan Kotun Koli da Gwamna Abba Ya Yi Rashin Nasara

Jigon NNPP Ya Fadi Abu 1 da Zai Faru da Alkalan Kotun Koli da Gwamna Abba Ya Yi Rashin Nasara

  • Buba Galadima ya yi magana kan nasarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu a Kotun Ƙolin ƙasar nan
  • Jigon na jam'iyyar NNPP ya bayyana cewa da gwamnan ya yi rashin nasara da ƴan Najeriya sun jefi alƙalan Kotun Ƙolin
  • Buba ya yi nuni da cewa ba gwamnan ya kamata a taya murna ba, sai dai alƙalan kotun saboda dawo da martabar ɓangaren shari'a

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wani jigo a jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Buba Galadima, ya ce da ƴan Najeriya sun jefi alƙalan kotun koli a kan tituna da sun kori Gwamna Abba Kabiru Yusuf na jihar Kano.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Kotun Ƙolin ta yanke hukunci a kan taƙaddamar shari'ar zaɓen gwamnoni takwas, inda ta soke hukuncin da ƙananan kotunan suka yanke a ƙararraki uku.

Kara karanta wannan

Kotun koli ta yanke hukuncin ƙarshe kan ƙarar da aka nemi tsige gwamnan PDP daga mulki

Buba Galadima ya yi magana kan nasarar Gwamna Abba
Buba Galadima ya ce alkalan Kotun Koli da sun sha jifa da ba Gwamna Abba ya yi nasara ba Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Daga cikin ƙararrakin guda takwas, na gwamnonin jihohin Zamfara, Kano da Plateau ne kaɗai Kotun Ƙolin ta sauya korar da kotun ɗaukaka ƙara ta yi musu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane abu ne zai faru da alƙalan Kotun Ƙolin?

Jaridar Daily Trust ta ce da yake magana a gidan Talabijin na Channels tv a shirin Sunday Politics, Galadima ya bayyana cewa:

"Bari na fara taya Kotun Koli murnar dawo da martabar ɓangaren shari’a. Taya murnar ba na NNPP ba ne ko Gwamna Abba ba, na Kotun Koli ne.
"Idan da sun yanke hukunci akasin haka, da an jefe su a kan titunan Najeriya kuma babu wanda zai iya tuƙa mota ɗauke da tambarin Kotun Ƙolin Najeriya.
"Da an rasa ƙwarin gwiwa a ɓangaren shari’a kuma ba na tunanin kowa zai yi mafarkin ya je kotu domin neman haƙƙinsa, domin kotun ra’ayin jama’a a duniya ta nuna cewa nasarar da Abba ya samu ta gaskiya ce."

Kara karanta wannan

Bayan hukuncin Kano da Plateau Kotun Koli ta tanadi hukunci kan karar neman tsige gwamnan PDP

Ya yi iƙirarin cewa a zaɓen 2023, wuri ɗaya kawai aka yi zabe shi ne Kano, ya ƙara da cewa jam'iyyar APC ta yi duk mai yiwiwa domin ta ci Kano.

Tinubu Ya Yi Watsi da Bukatar Ganduje

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, ya bayyana cewa Abdullahi Umar Ganduje, ya so APC ta yi nasara Kano.

Gwamnan ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya ƙi amincewa da buƙatar Ganduje na ganin an ba APC nasara a kotun ƙoli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel