Tashin Hankali a Abuja Yayin da Aka Kai Hari Wata Rugar Fulani, an Kashe Makiyaya Biyu

Tashin Hankali a Abuja Yayin da Aka Kai Hari Wata Rugar Fulani, an Kashe Makiyaya Biyu

  • Wasu da ba a san ko su waye ba sun kai harin ramuwar gayya a wata rugar Fulani a garin Kpache, karamar hukumar Abaja da ke birnin Abuja
  • A yayin harin, makiyaya biyun sun gamu da ajalinsu, yayin da wata majiya a rundunar 'yan sanda ta tabbatar da kai harin a daren ranar Talata
  • Rahotanni sun bayyana cewa wannan harin ya biyo bayan wata hatsaniya da aka samu tsakanin Fulani da 'yan sa kai da ya kai ga ajalin wani dan sa kai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Rahoto ya nuna cewa an kashe makiyaya biyu a wani harin ramuwar gayya da aka kai rugar Fulani a garin Kpache da ke gundumar Yaba, karamar hukumar Abaja, birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Bikin Kirsimeti: Yan sanda sun gano bindigu an boye su cikin buhu a wata jihar Kudu

City & Crime ta ruwaito cewa an yi hatsaniya tsakanin 'yan sakai da makiyayan a kasuwar Yaba a ranar Asabar wanda ya kai ga kashe dan sa kai daya, daga kabilar Bassa.

An kashe makiyaya biyu a sabon hari wata rugar fulani a Abuja
Majiyar rundunar 'yan sanda ta ce an kai hari wata rugar Fulani a Abuja, an kashe makiyaya biyu. Hoto: @NGPolice
Asali: Twitter

Sulhu tsakanin makiyaya da 'yan sa kai bai yi tasiri ba

Wani mazaunin Yaba, Saidu Shuaibu, wanda ya tabbatar da kashe makiyayan biyu a rugarsu da ke garin Kpache, ya shaidawa Daily Trust cewa an kai harin misalin karfe 11 na ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wadanda suka kai harin sun dira rugar Fulanin inda suka harbe makiyaya biyu har lahira, wanda ya jefa gaba daya yankin cikin tashin hankali.

Saidu Shuaibu ya ce:

"An kai wannan farmakin ne jim kadan bayan da shugaban karamar hukumar Alhaji Abubakar Umar Abdullahi ya je Yaba ranar Lahadi ya yi zaman sulhu da bangarorin biyu."

Abin da rundunar 'yan sanda suka ce kan harin

Kara karanta wannan

Tsaka mai wuya: Saurayi ya kashe budurwarsa bayan ta nemi ya biya ta kudin gamsar da shi

Wata majiya daga rundunar 'yan sandan Yaba wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da kashe makiyaya biyu a rugarsu da ke garin Kpache a daren ranar Talata.

Ya ce:

"Duk da cewa shugaban karamar hukumar ya ba da tabbacin zaman lafiya, wasu da ba a san ko su waye ba suka farmaki rugar Fulanin inda suka kashe makiyaya biyu."

Ya ce rundunar 'yan sanda ta je rugar a safiyar ranar Laraba don duba abin da ya faru, daga bisani ta kai rahoto ga babban ofishin hukumar na birnin Abuja.

Kakakin rundunar 'yan sandan birnin Abuja SP Adeh Josephine, ba ta ce uffan kan harin ba duk da aika mata sakonni a wayarta.

Kotu ta garkame matashin da ya kashe mahaifinsa a Kwara

A wani labarin, wata kotun majistire mai zama a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ta garkame wani matashi da ya kashe mahaifinsa kan yana yi masa fada.

Jami'in rundunar 'yan sanda da ya shigar da karar, Sajan Abdullah Sanni ya ce matashin ya tsere zuwa tsaunin garin Share bayan kashe mahaifinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel