Yan Sanda Sun Gurfanar da Wani Mutum da Ya Kashe Mahaifinsa a Kwara

Yan Sanda Sun Gurfanar da Wani Mutum da Ya Kashe Mahaifinsa a Kwara

  • Wata kotun majistire mai zama a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ta garkame wani matashi da ya kashe mahaifinsa kan yana yi masa fada
  • Jami'in rundunar 'yan sanda da ya shigar da karar, Sajan Abdullah Sanni ya ce matashin ya tsere zuwa tsaunin garin Share bayan kashe mahaifinsa
  • Mai shari'ar kotun Alhaji Mohammed Dasuki ya amince da bukatar Sajan Sanni na hana belin Saidi, inda ya dage shari'ar zuwa Janairu, 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kwara - Rundunar 'yan sanda ta gurfanar da Saidi Musa a gaban kotun majistire da ke jihar Kwara kan zargin kashe mahaifina, Chief Musa, sarkin Share a karamar hukumar Ifelodun da ke jihar.

Kara karanta wannan

Yan sandan Kano sun kama tubabben dan fashi da makami, suna neman wasu 72 ruwa a jallo

Ana zargin basaraken ya yi wa Saidi fada tare da zaginsa kan wani lamari da ba a sani ba, hakan ya bata ran matashin, inda ya sanya adda ya farmaki mahaifin.

Matashi ya kashe mahaifinsa saboda ya zage shi a Kwara
Yan sanda sun gurfanar da wani matashi da ya kashe mahaifinsa saboda ya zage shi a Kwara. Hoto: @NGPolice
Asali: Twitter

Rundunar 'yan sandan ta gurfanar da Saidi gaban kotun don a yanke masa hukuncin laifin kisan kai, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukuncin da kotu ta yanke kan Saidi

A cewar jami'i mai shigar da kara Sajan Abdullah Sanni, ya ce:

"Rahoton farko na 'yan sanda (FIR) ya nuna cewa Saidi ya harzuka da zagin da mahaifinsa yake yi masa, hakan ya sa ya sarrashi a kai da adda har ya mutu, sannan ya tsere zuwa tsaunin Share."

Radio Nigeria ya ruwaito jami'i mai shigar da karar na shaidawa kotun cewa laifin ba ya bukatar beli tunda kisan kai ne, tare da neman kotu ta garkame mai laifin har zuwa kammala shari'ar.

Kara karanta wannan

Ni na taimaki APC ta ci mulki, gwamnan Arewa ya soki 'yan Majalisar Tarayya da Suka Sako Shi a Gaba

Mai shari'ar kotun, Alhaji Mohammed Dasuki, a hukuncin da ya yanke, ya ba da ajiyar Saidi a gidan gyaran hali har zuwa ranar 9 ga watan Janairu, 2024 don ci gaba da shari'ar.

Sufetan 'yan sanda ya kashe abokin aikinsa, shi ma ya kashe kansa

A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta kawo maku labarin wani sufetan 'yan sanda ya bindige kansa bayan harbe abokin aikinsa har lahira a jihar Rivers.

Rahotanni sun bayyana cewa, Sufeta Nelson Abuante ya harbi Sufeta Monday Gbramana bisa kuskure yayin kama wani laifi, amma ganin danyen aikin da ya yi, shi ma ya kashe kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel