An kashe Makiyaya 7, wani 1 ya bace a sabon harin da aka kai a Jihar Filato

An kashe Makiyaya 7, wani 1 ya bace a sabon harin da aka kai a Jihar Filato

- An kashe Makiyaya bakwai a hare-haren da aka kai a Filato kwanan nan

- Miyagu sun hallaka Makiyaya, sun kuma ji wa dabbobinsu rauni a Bassa

- Rahotanni su na cewa wannan ne harin farko da aka kai a cikin wata hudu

Akalla makiyaya Fulani bakwai aka kashe a wasu mabambantan hare-hare biyu da aka kai a wani kauye da ake kira Maiyanga a jihar Filato.

Daily Trust ta ce kauyen ya na cikinyankin Kwall, a karamar hukumar Bassaa da ke jihar ta Filato.

Shugaban kungiyar Miyyeti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), na reshen jihar Filato, Nura Abdullahi, ya tabbatar da lamarin.

Alhaji Nura Abdullahi ya shaida wa ‘yan jarida a Jos cewa an kai wa makiyaya hari a Talatar da ta wuce, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyar.

KU KARANTA: Wuta ta ci mutum 6 a Abuja

Wani makiyayi daya ya bace ba a san inda ya shiga ba bayan wannan hari, bayan haka miyagun da su ka kai wannan hari sun kashe daruruwan shanu.

Kamar yadda shugaban kungiyar makiyayan ya bayyana, an yi amfani da makamai, an raunata dabbobi a harin da aka kai wa mutanensa a Maiyanga.

Alhaji Abdullahi ya tabbatar wa manema labarai sun sanar da jami’an ‘yan sanda da dakarun sojojin Operation Safe Haven game da mummunar ta’asar.

“Bayan harin na ranar Talata, makon da ya wuce, an yi wuf an kashe wasu makiyaya biyu da su ke kiwon shanunsu a yankin.” Inji shugaban MACBAN.

An kashe Makiyaya 7, wani 1 ya bace a sabon harin da aka kai a Jihar Filato
Gwamnan Filato Simon Lalong Hoto: www.thisdaylive.com
Source: UGC

KU KARANTA: Za a kori masu talla daga Legas

“Mun kai kara wajen Operation Safe Haven, kuma mu ka roki shugabannin kungiyar Miyyeti Allah su yi hakuri, yayin da ake binciko wanda su ka yi barnar.”

“Abin mamaki a makon nan, an sake kashe makiyaya da ke kiwo a wannan wurin dai. Ba su shiga gonar kowa ba, cikin duwatsu ne, amma aka bi aka kashe su.”

A makon nan ne mu ka samu rahoto cewa 'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kai wa dakarun 'yan sandan Najeriya wani hari a cikin jihar Borno.

'Yan ta'addan sun yi nasarar karbe wasu motocin jami'an tsaro biyu a harin da su ka kai.

Rahotanni sun ce kungiyar ta'addan Boko Haram ISWAP, masu lakabi da Jamā'at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wa'l-Jihād, sun ragargaza motocin jami'an tsaron.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel