Tsaka Mai Wuya: Saurayi Ya Kashe Budurwarsa Bayan Ta Nemi Ya Biya Ta Kudin Gamsar da Shi

Tsaka Mai Wuya: Saurayi Ya Kashe Budurwarsa Bayan Ta Nemi Ya Biya Ta Kudin Gamsar da Shi

  • Wani matashi mai shekara 19 Muhammad Ibrahim ya kashe budurwarsa saboda ta nemi ya biya naira dubu biyar bayan ta biya masa bukatarsa
  • Hatsaniya kan biyan kudin ta kaure tsakanin masoyan har ta kai ga doki in doke ka, abin ya zo da karar kwana Ibrahim ya daba wa budurwar wuka
  • Duk da kokarin jama'a na ceton budurwar, rai ya yi halinsa, inda shi ma Ibrahim ya gamu da fushin mutane, amma 'yan sanda suka cece shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Bauchi - Rundunar 'yan sanda ta ce wani dan shekara 19 Muhammad Ibrahim a jihar Bauchi ya kashe budurwarsa Emmanuella Ande kan naira dubu biyar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai sabon farmaki kauyen Sokoto, sun yi mummunar barna

Kakakin rundunar jihar SP Ahmed Mohammad Wakil ya ce budurwar ta nemi kudin daga hannun saurayin bayan wata bukata da ta biya masa, shi kuma ya hana ta.

Matashi ya kashe budurwarsa kan N5,000 a Bauchi
Rundunar 'yan sanda ta cafke matashin da ya kashe budurwarsa kan N5,000 a jihar Bauchi. Hoto: Nigerian Police
Asali: Twitter

A ranar Laraba ne 'yan sanda suka kama matashin, bayan da ya caka wa budurwar wuka a kahon zuci a wani dakin da ta kama a 'Bayan Gari', inda mutane su ka jiyo ihunta suka kai dauki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashin ya amsa laifinsa, za a gurfanar da shi gaban koliya

A kokarin jama'a na balle kofar dakin, matashin ya caka wa wani Zaharaddeen Adamu wuka a hannu, amma dai mutane suka fara nada wa matashin na jaki, rahoton Daily Trust.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce jami'an atisayen wanzar da zaman lafiya sun je 'Bayan Gari' inda suka ceci matashin daga hannun fusatattun jama'ar, tare da daukar gawar budurwar.

Kara karanta wannan

Mu leka kotu: Dan kasuwa ya nemi naira miliyan 1 daga hannun matarsa kafin ya sake ta

Wakil ya ce:

"Bayan tuhumar Ibrahim, ya amsa laifin kashe budurwar, inda ya bayyana cewa ya hadu da ita a Facebook kuma sun sha soyayya har ya saci kudin mahaifinsa ya je Fatakwal don su gana."

Jami'in dan sandan ya ce an gano wuka a hannun matashin, yayin da rundunar ke ci gaba da bincike inda za ta gurfanar da shi gaban koliya nan ba da jimawa ba.

Sufetan 'yan sanda ya kashe kansa bayan bindige abokin aikinsa

A wani labarin, wani Sufeto a rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ya kashe kansa bayan da aka ce ya harbe abokin aikinsa Monday Gbaramana har lahira.

Rahotanni sun bayyana cewa dan sandan mai suna Sufeto Nelson Abuante ya harbe abokin aikinsa a ranar Lahadi a Nyogor-Lueku da ke karamar hukumar Khana a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.